Daga Fitowa Takarar Sanata, an Mika Bello Badejo ga EFCC bayan Cafke Shi
- Jami’an tsaro sun kama Bello Bodejo a Jalingo tare da mika shi ga Economic and Financial Crimes Commission domin ci gaba da bincike
- Mataimakin Bello Bodejo ya ce har yanzu ba a sanar da iyalansa laifin da ake zarginsa da aikatawa ba bayan an kai shi Abuja
- Hadimin dan takarar ya zargi wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa a Taraba da shirya kamun domin hana shi shiga tantancewar ‘yan takarar APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo ya sake shga wata matsala bayan jami'an tsaro sun cafke shi a jihar Taraba.
An kama Bodejo ne wanda ke neman takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya karkashin jam’iyyar APC a Jalingo da ke jihar.

Source: Facebook
Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke Bodejo ne bayan ya isa filin jirgin saman Danbaba Suntai da ke Jalingo a daren ranar Alhamis.
Daga bisani, jami'an tsaron sun mika shi ga jami’an hukumar yaki da cin hanci a Najeriya domin ci gaba da bincike.
Mataimakinsa, Malam Umar, ya ce an dauke shi zuwa Abuja bayan kama shi, inda aka mika shi ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike.
Ya bayyana cewa har yanzu iyalan Bodejo ba su san irin laifin da ake zarginsa da aikatawa ba, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin magoya bayansa.
Malam Umar ya yi zargin cewa kamun yana da nasaba da yadda Bodejo ke samun karbuwa a siyasar yankin Sanatan Taraba ta Tsakiya.
A cikin bayansansa, Malam Umar ya ce:
“Yayin da nake magana da kai yanzu haka, ana dab da kammala tantance masu neman takarar gwamna da kujerun majalisar dattawa da ta wakilai, kuma manufar wadanda suka shirya kama shi ita ce hana shi shiga aikin tantancewar.”
Ya kuma zargi wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa a jihar da hannu wajen shirya kama shi domin hana shi shiga tantancewar ‘yan takarar kujerun gwamnoni, Sanata da Majalisar Wakilai.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da gudanar da tantancewar ‘yan takarar APC yayin da magoya bayan Bodejo ke nuna damuwa kan makomar takararsa.
Ya kuma zargi wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa a jihar da hannu wajen shirya kama shi domin hana shi shiga tantancewar ‘yan takarar kujerun gwamnoni, Sanata da Majalisar Wakilai.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da gudanar da tantancewar ‘yan takarar APC yayin da magoya bayan Bodejo ke nuna damuwa kan makomar takararsa.
Za a tsare Bodejo na watanni 2
A wani labarin, an ji cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo zai ci gaba da zama a hannun hukumomin tsaron kasar nan.
Wannan ya biyo bayan hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya, Mai Shari'a Emeka Nwite ya yanke kan bukatar DIA.
Hukumar leken asirin sojin kasar nan ta shigar da Bodejo kara bisa zargin ta'addanci da kai wa sojoji hari a Nasarawa.
Asali: Legit.ng

