Pantami Ya Bayyana Muhimmancin Zaben Fitar da Gwani ga Jam'iyyar APC, Ya Yi Gargadi

Pantami Ya Bayyana Muhimmancin Zaben Fitar da Gwani ga Jam'iyyar APC, Ya Yi Gargadi

  • Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana a gaban kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na APC
  • Farfesa Pantami bayan kammala tantancewar ya yi magana kan makomar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Tsohon Ministan ya nuna cewa dole ne a gudanar da zaben fitar da gwani sahihi kuma wanda yake cike da adalci

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya gargaɗi jam’iyyar APC kan zaben fitar da gwani na gwamnan Gombe.

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa sahihancin zaɓen fitar da gwani na takarar gwamna a jihar Gombe ne zai nuna ƙarfin jam’iyyar na cikin gida, sannan ya nuna irin amincewar da jama’a ke da ita ga dimokuraɗiyya.

Pantami ya yi magana kan makomar APC
Farfesa Isa Ali Pantami na jawabi a wajen taro Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala tantance masu neman takarar gwamna na APC da aka gudanar a gidan gwamnan jihar Kaduna da ke Asokoro, Abuja a ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ya fadi matsayar APC kan zaben fitar da gwani a Yobe

Me Pantami ya ce kan zaben fitar da gwani?

Pantami, wanda yake sahun gaba wajen adawa da tsarin maslaha da aka yi a Gombe, ya ce gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin adalci kuma ba tare da tsoma baki ba, yana da matuƙar mahimmanci idan har APC tana fatan kiyaye mutuncinta.

Gargaɗin na Pantami na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da takaddama kan amincewa da Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha a Gombe, tsarin da tun farko Pantami ya bayyana a matsayin “wasan kwaikwayo” tare da shan alwashin cewa zai yaƙi lamarin ta hanyar da “ba a taɓa gani ba”.

Yayin tantancewar a Abuja, Pantami ya bayyana cewa matakin da shugabancin jam’iyya na ƙasa ya ɗauka na tantance dukkan masu neman takara ya nuna cewa har yanzu jam’iyyar tana da damar nuna adalci a cikinta.

“Tun da aka gayyace mu don tantancewa, hakan yana nuni da cewa jam’iyyar a matakin ƙasa ta ba wa kowane ɗan Najeriya dama ta adalci."

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama yayin da APC ta tantance gwamnoni 14 babu sunan Fubara

- Farfesa Isa Ali Pantami

Me Pantami ya ce kan makomar APC?

Tsohon Ministan ya jaddada cewa wanzuwar APC a matsayin tsarin siyasa ya dogara ne kacokan kan ko mambobinta da jama’a za su kalli tsarin gudanarwarta na cikin gida a matsayin sahihi.

Ya ƙara da cewa dimokuraɗiyyar cikin gida da adalci suna da matuƙar mahimmanci ga dorewar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Pantami ya yi magana kan makomar APC
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Twitter

A cewarsa, zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato zai iya ƙarfafa jam’iyyar ne kawai idan har an gudanar da shi cikin adalci kuma ba tare da maguɗi ba.

“Dole ne zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ya kasance sahihi, cikin adalci, kuma ba tare da tsoma baki ba. Duk wanda yake da wani son zuciya bai kamata a bar shi ya jagoranci tsarin ba."

- Farfesa Isa Ali Pantami

Sanatan APC ya koma PDP a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Gombe ta Kudu a majalisar dattawa, Anthony Siyako Yaro, ya fice daga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Sanata Anthony Siyako Yaro ya sanar da komawarsa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP wadda ya yi takara a karkashinta a 2023.

Ficewar sanatan daga APC dai na zuwa ne bayan ya rasa tikitin takarar jam'iyyar domin sake komawa kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng