Babbar Magana: Sowore Ya Yi Maganar da Za Ta Tayar da Hankalin Tinubu, Atiku kan Zaben 2027

Babbar Magana: Sowore Ya Yi Maganar da Za Ta Tayar da Hankalin Tinubu, Atiku kan Zaben 2027

  • Dan takarar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben shugaban kasa na 2027
  • Sowore ya ce bayan zaben, Bola Tinubu da Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi, ba za su ci gaba da rike mukamansu ba
  • DSS ta nemi dage shari’ar Sowore har bayan zaben domin bai wa dan takarar damar gudanar da yakin neman zabensa ba tare da cikas ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya bayyana cewa zai zama shugaban Najeriya bayan babban zaben 2027.

Sowore ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake martani kan matakin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) na neman dage karar da take yi masa har zuwa bayan zaben shugaban kasa na 2027.

Sowore ya ce zai ci zaben 2027
Omoyele Sowore da ke takarar shugaban kasa a zaben 2027 Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Sowore: DSS ta dakatar da kararta kan dan takarar shugaban kasa, an ji dalili

DSS ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde, SAN, da ya nemi kotu ta dage sauraron karar, domin bai wa Sowore damar shiga harkokin zabe ba tare da shari’ar ta kawo masa cikas ba.

Sowore ya yi hasashen sauyin gwamnati

Da yake mayar da martani, Sowore ya ce ba za a sake ci gaba da shari’ar bayan zaben ba saboda a ganinsa Shugaba Bola Tinubu da Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi, ba za su kasance a mukamansu ba.

Ya zargi gwamnatin da amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa abokan hamayyar siyasa lamba.

“Bayan zaben 2027, Sowore zai zama shugaban Najeriya. Babu ja da baya,” in ji shi.

Sowore ya kara da cewa zai kawo karshen abin da ya kira tsangwamar siyasa da kuma amfani da hukumomin gwamnati wajen yakar abokan hamayya.

Ya kuma ce wadanda suka yi amfani da hukumomin gwamnati wajen cin zarafin abokan hamayyar siyasa za su fuskanci alhakin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Kofa ya ce APC za ta lashe Kano baki daya, Kwankwaso zai rasa kujeru a 2027

Asalin karar DSS kan Sowore

Shari’ar DSS ta samo asali ne daga wasu sakonnin da Sowore ya wallafa a kafafen sada zumunta a watan Agusta 2025.

A cikin sakonnin, ya kira Shugaba Tinubu da kalmar “mai laifi”, lamarin da ya sa DSS ta garzaya babbar kotun tarayya domin neman fassarar kotu kan ko irin wannan magana ta kai matsayin laifin cin zarafin mutum ta kafafen sadarwa.

Hukumar ta kuma nemi kotu ta tantance halaccin amfani da irin wannan kalma wajen bayyana shugaban kasa ko wani mutum a bainar jama’a.

Sowore ya yi magana kan zaben 2027
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Za a gabatar da bukatar dage shari’ar

Ana sa ran DSS za ta gabatar da bukatar dage sauraron karar a hukumance ga babbar kotun tarayya lokacin da kotun ta koma zaman yau da kullum.

Ana sa ran kotun za ta koma zaman bayan hutun shekara-shekara na bangaren shari’a a ranar 14 ga Satumba, 2026.

Matakin DSS na neman dage shari’ar ya zo ne yayin da ake kara samun shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai

Matsayar Sowore kan dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC) a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya bayyana matsayarsa kan dawo da tallafin man fetur.

Omoyele Sowere ya ce zai maido da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng