Tirkashi: APC Ta Dauka da Zafi bayan Atiku Ya Yi Wasu Kalamai
- APC ta soki Atiku Abubakar kan zargin cewa masu mulki sun “sace tattalin arzikin Najeriya” bayan sun sace zaɓen 2023
- Jam’iyyar ta bukaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gabatar da hujjoji a kotu idan yana da tabbacin cewa an aikata laifuka
- APC ta ce waɗanda aka zaɓa suna da ikon kundin tsarin mulki na amfani da albarkatun ƙasa wajen aiwatar da manufofin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, kan zargin cewa masu mulki sun “sace tattalin arzikin Najeriya”.
Atiku, wanda ke fafatawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ya zargi gwamnatin APC da ƙara tsananta wa ‘yan Najeriya wahalhalun tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, Bola Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC a Aso Rock

Source: Facebook
Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Leadership.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a daren Talata yayin da yake jawabi ga magoya bayansa.
APC ta ce Atiku ya je kotu
Bala Ibrahim ya bukaci Atiku da ya gabatar da hujjojin zarge-zargen nasa a kotu maimakon yin zarge-zarge ga gwamnati da jami'anta.
Ya ce idan Atiku na da yakinin cewa an aikata laifuka, ya kamata ya kai ƙarar lamarin gaban kotu domin a binciki zarge-zargen.
“Idan yana da yakini kan tsarin shari’a, ya kamata ya je kotu ya tabbatar da zarge-zargen da ya yi kan mutanen da yake fafatawa da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bai kamata a riƙa zargin mutane da aikata laifuffuka ba tare da gabatar da hujjoji ba.
“Idan ka zargi wasu mutane da aikata laifi kuma ka yi imani da tsarin shari’a, kada kawai ka yi zargin, ka je kotu ka tabbatar da abin da ka faɗa,” in ji shi.
“Ya bayyana abin da yake nufi”
Bala Ibrahim ya kuma nemi Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan abin da yake nufi da cewa an “sace tattalin arzikin Najeriya”.
Ya tambayi ko Atiku na nufin cewa gwamnati tana yin abubuwa ne da suka saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, ko kuma yana nufin cewa jami’an gwamnati ba su da ikon amfani da albarkatun ƙasa wajen aiwatar da manufofi.
“Dole ne ya bayyana ainihin abin da yake nufi. Ba za ka yi irin wannan zargi na gama-gari ba tare da hujja ba,” in ji shi.
APC ta kare ikon gwamnati kan albarkatun kasa
Daraktan yaɗa labaran jam’iyyar ya ce gwamnatin da aka zaɓa tana da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta na amfani da albarkatun ƙasar wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da aka tsara domin amfanin jama’a.
Ya ce saboda haka, ba za a iya bayyana duk wani kashe kuɗin gwamnati a matsayin “sata” ba tare da an gabatar da hujjar cewa an aikata laifi ba.
“Duk wanda aka zaɓa ya yi wa jama’a hidima an ba shi iko da hurumin amfani da albarkatun ƙasar da ofishin da yake riƙe da shi wajen yin abubuwan da za su amfani jama’a,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Atiku ya kamata ya gabatar da hujjoji idan yana da tabbacin cewa an aikata laifukan da ya ambata, domin a tantance su ta hanyar da doka ta tanada.

Source: Facebook
Amaechi ya yi magana kan tsarin Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur.
Amaechi ya ce shirin Atiku Abubakar, na tallafin man fetur ba wai komawa tsohon tsarin tallafin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ba ne.
Asali: Legit.ng

