Rikicin Yobe: Mutum 6 da Aka Hana Takarar Gwamna a APC Sun Gana da Kashim Shettima

Rikicin Yobe: Mutum 6 da Aka Hana Takarar Gwamna a APC Sun Gana da Kashim Shettima

  • Mutane shida da ke neman takarar gwamnan jihar Yobe a inuwar APC sun gana da Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima
  • Wannan ganawa na zuwa ne bayan rikicin da ya barke a APC reshen jihar Yobe kan wanda zai gaji Gwamna Mai Mala Buni a Mayun 2027
  • Rahotanni sun ce an gudanar da ganawar ne a gidan mataimakin shugaban kasa da ke Abuja cikin sirri, inda aka tattauna abubuwa da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe, Nigeria - Masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Yobe har su shida sun gana da Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a gidansa da ke Abuja.

Wadannan 'yan takara sun ziyarci Shettima ne kan rikicin da ya dabaibaye batun magajin Gwamna Mai Mala Buni, wanda shi zai yi wa APC takarar gwamna a zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yana jagorantar taron NEC a Aso Rock, Abuja Hoto: @OfficialSKSM
Source: Twitter

Masu neman takara sun hadu da Kashim Shettima

Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar 'yan takarar ta kunshi Sanata Muhammad Ibrahim Bomai mai wakiltar Yobe ta Kudu, Lawan Kolo Geidam tsohon shugaban hukumar NEMA, da Injiniya Mustapha Maihaja.

Sauran sun hada da tsohon sufeto janar na ’yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, Kashim Musa Tumba da Bashir Machina.

Masu son tikitin APC sun gana boye

Rahotanni sun ce an gudanar da ganawar ne a gidan mataimakin shugaban kasa da ke Abuja cikin sirri.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takaddama kan fitar da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, a matsayin wanda APC ke so ya zama 'dan takarar gwamna.

Majiyoyi sun bayyana cewa tattaunawar ta fi mayar da hankali ne kan yadda za a samu mafita cikin lumana da amincewar kowa game da rikicin.

Kashim Shettima ya bukaci a sasanta

Kara karanta wannan

Abba ya yi tattaki zuwa Abuja, ya mika fam neman takarar gwamnan Kano

A cewar sanarwar bayan taron, Shettima ya bukaci tawagar ’yan takarar da aka fi sani da G-6 da ta sake nazarin matsayinta kan adawa da tsarin da aka bi wajen tsaida Baba Malam Wali.

Ya kuma bukace su da su rungumi tattaunawa domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yan takarar Yobe.
Masu neman takarar gwamnan Yobe tare da Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a gidansa na Abuja Hoto: Auwal Hussaini
Source: Facebook

Abin da aka amince da shi a ganawar

A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan taron, ’yan takarar sun bayyana ganawar a matsayin mai amfani, tare da cewa za a ci gaba da tuntuba domin warware matsalar cikin lumana.

“Mun tattauna halin da ake ciki game da zaben dan takarar gwamna na APC a jihar Yobe da kuma bukatar samun mafita mai dorewa,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa an cimma matsaya kan ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin yin sulhu da dukkan ’yan takara bakwai za su amince da shi ko kuma gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana.

Takarar gwamnan APC a Yobe ta tada kura

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya shiga takarar gwamnan jihar Yobe.

Kara karanta wannan

2027: Shettima na so Sanata Wadada ya zama gwamnan Nasarawa

Majiyoyi sun ce tsohon ɗan sandan ya shiga tafiyar ne bayan matsalar da aka samu a shirin samar da ɗan takara ta hanyar sasanci tsakanin masu neman kujera.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Mai Mala Buni ya tsayar da wanda ya ke so ya gaje shi a matsayin gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262