Sowore: DSS Ta Dakatar da Kararta kan dan Takarar Shugaban Kasa, an Ji Dalili

Sowore: DSS Ta Dakatar da Kararta kan dan Takarar Shugaban Kasa, an Ji Dalili

  • DSS ta umarci lauyanta Akinlolu Kehinde, SAN, ya nemi kotu ta dage karar da ake yi wa Omoyele Sowore har bayan zaben 2027
  • Hukumar ta ce an dauki matakin ne domin bai wa Sowore damar shiga yakin neman zabe ba tare da shari’ar ta kawo masa cikas ba
  • Ana sa ran DSS za ta sanar da babbar kotun tarayya a hukumance kan matakin daga ranar 14 ga Satumba, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde, SAN, da ya nemi dage sauraron karar da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce DSS na son a dakatar da shari’ar har zuwa bayan zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Rundunar sojojin Najeriya ta gamu da gagarumar matsala da aka yi mata kutse

DSS ta dakatar da kararta kan Sowore
Jami'an DSS da dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore Hoto: @OfficialDSSNg, @yelesowore
Source: Twitter

A cewar majiyar, matakin zai bai wa Sowore damar shiga harkokin yakin neman zabe da sauran ayyukan siyasa ba tare da shari’ar ta zama cikas gare shi ba, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Yadda aka fara shari’ar

DSS ta shigar da karar ne kan wasu sakonnin da Sowore ya wallafa a shafukansa na X da Facebook a ranar 25 ga Agusta, 2025.

A cikin sakonnin, Sowore ya kira Shugaba Bola Tinubu da kalmar “mai laifi”, lamarin da ya sa DSS ta ba shi wa’adin kwanaki bakwai ya cire sakonnin.

Bayan wa’adin ya cika ba tare da an cire sakonnin ba, DSS ta garzaya babbar kotun tarayya a ranar 16 ga Satumba, 2025.

Hukumar ta nemi kotun ta yi hukunci kan ko ya halatta mutum ya kira shugaban kasa ko wani mutum “mai laifi” a bainar jama’a.

DSS ta ce dakatarwar ba ta shafi zabe kadai ba

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

Wata majiya kusa da tawagar lauyoyin DSS ta ce Darakta-Janar na hukumar, Tosin Ajayi, ya gana da babban lauyan da kuma manyan jami’an sashen shari’a na hukumar a ranar 20 ga Agusta.

Majiyar ta ce an tattauna yiwuwar dakatar da shari’ar ne bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage takunkumin da aka sanya kan fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2027.

“DSS ta ga cewa zai dace a dakatar da shari’ar domin bai wa Sowore damar shiga zaben mai zuwa ba tare da wata matsala ko cikas ba,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa Ajayi ya bayyana cewa shari’ar ta shafe kusan shekara guda a gaban kotu, kuma dakatar da ita na wasu watanni hudu ba zai haifar da wata babbar illa ba.

Za a sake duba wasu kararrakin

An kuma ce DSS ta umarci tawagar lauyoyinta da ta sake duba wasu kararraki makamantan wannan da suka shafi ‘yan takarar wasu mukamai a zaben 2027, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

A baya, hukumar ta bayyana cewa manufar shari’ar Sowore ita ce neman fassarar kotu kan halaccin kiran Shugaba Tinubu ko wani mutum da sunan “mai laifi”, ba wai hana Sowore gudanar da harkokin siyasarsa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Takarar Pantami ta gwamnan Gombe ta samu babban tagomashi

A cikin wata wasika da DSS ta aikewa shugaban Meta a ranar 6 ga Satumba, 2025, hukumar ta ce nauyin da doka ta dora mata na kare shugaban kasa ya wuce barazanar kai hari ta zahiri, ya hada da hare-haren da za su iya shafar tunaninsa.

Sowore ya samu sauki daga wajen DSS
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore Hoto: @yelesowore
Source: Facebook

Yaushe za a sanar da kotu?

Majiyar ta ce ana sa ran DSS za ta sanar da babbar kotun tarayya a hukumance kan matakin dakatar da shari’ar daga ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026.

A wannan rana ne ake sa ran kotun za ta koma zaman yau da kullum bayan kammala hutun shekara-shekara na bangaren shari’a.

Sowore, wanda a baya kotun ta bayar da belinsa bisa sanayya zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na siyasa yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.

Sowore zai dawo da tallafin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Omoyele Sowore ya ce cire tallafin ya ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng