Ta Fara Tsami a Kebbi tsakanin Gwamna da Malami bayan Sayan Fom Din Takara

Ta Fara Tsami a Kebbi tsakanin Gwamna da Malami bayan Sayan Fom Din Takara

  • Gwamnatin Kebbi ta zargi tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da munafuncin siyasa bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takara
  • Malami ya tabbatar da shirin tsayawa takarar gwamnan Kebbi a karkashin jam’iyyar ADC a 2027 da ake tunkara a kasar
  • Hadimin gwamna, Yahaya Sarki, ya ce matsalolin tsaro, talauci da durkushewar tattalin arziki sun karu a mulkin Muhammadu Buhari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Gwamnatin Kebbi ta caccaki tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami kan siyasa.

Hakan ya biyo bayan rahotannin cewa Malami ya shiga takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar ADC domin zaben 2027.

Gwamnatin Kebbi ta caccaki Malami
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi da Abubakar Malami. Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, Abubakar Malami SAN.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, ya fitar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Za a buga siyasa a Kebbi, Abubakar Malami ya sayi fom din takara na ADC

Gwamnatin Kebbi ta caccaki Abubakar Malami

Gwamnatin ta bayyana kalaman Malami a matsayin “munafukin siyasa,” tana zarginsa da taimakawa wajen jefa Kebbi da Najeriya cikin matsalolin da ake fama da su yanzu.

Sanarwar ta ce duk da cewa Malami na da ‘yancin neman mukami bisa kundin tsarin mulki, sukar da yake yi wa gwamnatin yanzu cike take da karya da kuma munafuncin siyasa.

Gwamnatin ta ce matsalolin rashin tsaro, talauci, durkushewar ilimi da wahalar tattalin arziki da Malami ya ambata a matsayin dalilin neman mulki, sun kara tsananta ne lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da ya yi aiki a cikinta.

Ta kuma zargi wasu tsofaffin jami’an gwamnatin tarayya da yin anfani da amanar jama’a wajen tara dukiya maimakon magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka addabi kasar nan tsakanin 2015 zuwa 2023.

Gwamnatin Kebbi ta soki Malami da munafurci
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi. Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
Source: Facebook

Gwamnatin Kebbi ta caccaki mulkin Buhari

Gwamnatin Kebbi ta kara da cewa Malami da abokan siyasarsa sun gaza daukar mataki mai karfi wajen dakile matsalar ‘yan bindiga da tabarbarewar rayuwar jama’a lokacin da suke mulki.

Kara karanta wannan

An saka sunan El Rufai, Ganduje da Malami kan zargin kisan Dadiyata

Sai dai gwamnatin ta kare ayyukan Gwamna Nasir Idris, tana cewa tun bayan hawansa mulki a 2023 an samu ci gaba a bangarorin ilimi, lafiya, noma, karfafawa matasa da kuma tsaro.

Ta ce an gina dubban dakunan karatu, an bude sababbin makarantu tare da rabon kayan koyarwa domin inganta ilimi a fadin jihar.

Haka kuma gwamnatin ta bayyana cewa an dauki malamai sama da 2,000 aiki tare da horas da karin ma’aikata domin bunkasa harkar ilimi.

A bangaren lafiya kuwa, gwamnatin ta ce ana gyaran manyan asibitoci 31 da ke fadin jihar, yayin da ayyuka suka kusa kammala a Birnin Kebbi, Argungu, Yauri, Zuru da Bunza.

2027: Gwamnatin Kebbi ta yi alkawari ga Tinubu

A baya, an ji cewa jam’iyyar APC a Kebbi ta shirya gagarumin gangamin hadin kai na mutum miliyan daya domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu.

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa dimbin jama’ar da suka halarta na nuna cewa al’ummar Kebbi suna tare da APC mai mulki.

Jami’an APC ciki har da sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da tsoffin gwamnoni sun halarci taron, inda suka nuna kwarin gwiwar samun kuri’u masu yawa a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.