INEC Ta Fitar da Sunayen Yan Takarar Gwamna na Jihohi a Zaben 2027, An Canza Wasu
- INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohin Najeriya, lamarin da ya jefa ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki cikin rudani
- Wasu ’yan takara sun yi mamakin ganin an cire sunayensu daga jerin da aka manna a ofisoshin hukumar INEC a jihohi
- A Nasarawa, dan takarar SDP Musa Adamu Angba ya ce a shirye yake ya sauka daga takarar domin goyon bayan tsohon Sufeto-Janar Mohammed Adamu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamna na duka jihohin Najeriya a zaben 2027.
’Yan takara da masu ruwa da tsaki a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban a Najeriya sun shiga fargaba bayan ganin sunayen da INEC ta fitar.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa yan takarar wasuu jam'iyyu da suka ci zaben fitar da gwani ba su ga sunayensu a cikin jerin ba, maimakon haka an maye gurbinsu da wasu daban.
Tuni dai ’yan takara da magoya bayansu suka fara zuwa ofisoshin hukumar da ke jihohi domin duba sunayensu.
INEC ta canza sunayen wasu yan takara
A jihar Adamawa, an sauya sunayen wadanda tun farko aka bayyana a matsayin ’yan takarar ADC, Ambasada Omar Suleiman, wanda aka fi sani da Omarana, da na PDP, Caleb Andrew.
An maye gurbin sunan dan takarar gwamnan ADC da sunan Hamman Tukur Modibbo Ribadu a jihar Adamawa
A jihar Neja kuwa, dan takarar gwamna na PDP, Abubakar Suleiman, ya amince ya janye daga takarar, yayin da dan takarar SDP a jihar Nasarawa ya nuna cewa shi ma zai iya mika tikitinsa.
Dan SDP zai sauka wa tsohon IGP
Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihar Nasarawa, amma babu sunayen wasu fitattun ’yan takara biyu, tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda (IGP), Mohammed Abubakar Adamu, da Sanatan Nasarawa ta Kudu, Mohammed Ogoshi Onawo.

Kara karanta wannan
Neja: Bayan umarnin Tinubu, an gano abin da yan sanda ke yi don ceto masallata da aka sace
A maimakon haka, an saka Musa Adamu Angba a matsayin dan takarar SDP, yayin da shugaban APM na jihar, Mohammed Awwal Suleiman, ya bayyana a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Da yake magana a wata hira, Angba ya ce a shirye yake ya mika tikitin SDP ga tsohon IGP Adamu “idan bukatar hakan ta taso”.
“Mutane suna taya ni murnar ganin sunana cikin jerin INEC. Ni kawai ina gode wa Allah da ya sa na samu kaina a wannan matsayi a yau,” in ji shi.
Da yake magana kan rade-radin yiwuwar sauya dan takarar, dan takarar SDP ya ce yana da kyakkyawar alaka da tsohon IGP Adamu.

Source: Twitter
“Mun yi magana. Na ji tausayinsa sosai saboda abin da aka yi masa. Idan ka ji ina cewa shi ne wanda zan yi amfani da shi wajen dawo da jihar Nasarawa kan turbar da ta dace, za mu iya mika masa al’amura,” in ji Angba.
Sai dai ya musanta cewa yana da masaniya kan wata rantsuwar da ake yadawa a kafafen sada zumunta da ke cewa ya amince ya janye daga takarar, kamar yadda Vanguard ta kawo.
INEC za ta dauki ma'aikatan wucin gadi
Kun ji cewa hukumar zaben Najeriya watau INEC ta ce za ta dauki kusan ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 a babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC , Farfesa Joash Amupitan, ya ce za a tura ma’aikatan wucin gadin zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 da ke faɗin ƙasar.
Asali: Legit.ng

