Khamenei Ya Tuna Ranar Haihuwar Annabi SAW, Ya ba Kasashen Musulmi Shawara
- Jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei, ya fitar da sanarwa inda yake shawartar shugabannin kasashen Larabawa
- Khamenei ya ce rarrabuwar kan Musulmi na amfanar makiyansu, yana mai kira ga hadin gwiwa, taimakon juna da kare kansu
- Kiran ya zo ne yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin Iran da kasashen Gulf, bayan Tehran ta kai hare-hare kan wasu sojin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Shugaban koli na Iran, Mojtaba Khamenei, ya ba shugabannin kasashen Musulmi shawarakan hadin kai.
Khamenei ya bukaci kasashen Musulmi, musamman wadanda ke yankin Gulf, su hada kai domin fuskantar abin da ya kira “ainihin makiyinsu”.

Source: Getty Images
Khamenei ya bayyana hakan ne cikin wani sako domin hadin kan Musulmi, wanda ake gudanarwa domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad, cewar Al Jazeera.
A cikin sakon, ya yi kira ga hadin kan Musulmi, da yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban, tare da taimakon juna wajen kare kai daga barazana
Ya ce duk wanda ke haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi, ko da da gangan ne ko ba da gangan ba, yana taimaka wa makiyan Musulunci.
Khamenei ya tambayi ko da gaske ne da an samu hadin kan Musulmi, da an bar Falasdinawa cikin irin wannan halin rashin taimako.
Tun bayan harin sama da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran watanni shida da suka gabata, ba a sake ganin Khamenei a bainar jama’a ba.
An ce ya samu raunuka a hare-haren, wadanda suka haddasa yakin Iran tare da kashe mahaifinsa kuma tsohon shugaban koli, Ayatollah Ali Khamenei.
Kiran da Khamenei ya yi na hadin kai ya yi kama da wani sako da ya gabatar wa ’yan Iran ranar Juma’a kan bukatar kare hadin kan al’umma,
A wancan sakon, ya ce ya hana duk wani mataki da ka iya cutar da hadin kan al’umma, sannan ya bukaci hukumomi su guji kalaman da za su raunana kwarin gwiwar kasa.
Khamenei ya kuma tambayi sarakunan kasashen Larabawa na Gulf ko “’yan daba marasa asali” za su iya kwadayin kasashensu da dukiyoyinsu idan al’ummomi da gwamnatocin Gulf sun kasance cikin hadin kai.
Ya ce hadin kan kasashen Gulf karkashin tutar Musulunci zai taimaka wajen kare su daga barazanar waje da kuma kare kadarorinsu.
Tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979, masarautun kasashen Larabawa na Gulf sun dauki akidar juyin juya halin Iran a matsayin barazana ga tsarin siyasarsu.
Sun kuma nuna damuwa kan kalaman Iran masu adawa da tsarin sarauta da kuma tasirinta na siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
A yayin rikicin da ake ciki, Tehran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da wasu ababen more rayuwa a kasashen Gulf, lamarin da ya kara nuna tsananin rashin jituwa.
Khamenei ya ce:
“Shawarata mai karfi kuma mai maimaituwa ga shugabannin kasashen Musulunci, musamman kasashen Yammacin Asiya da Gulf, ita ce ku gano ainihin makiyinku, ku fahimci shirinsa kuma ku tunkare shi.”
'Iran ba za ta yafewa Amurka ba'
An ji cewa Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba za ta taɓa mantawa ko yafe harin makarantar Minab ba.
Araghchi ya bayyana ɗaliban da aka kashe a harin a matsayin “jarumai” ga Iran, yayin da ake ci gaba da tunawa da su.
Mahukuntan Iran sun zargi Amurka da kai harin, yayin da Washington da Isra’ila ba su amince da alhakin kai harin ba.
Asali: Legit.ng


