Zulum Ya Gwangwaje Mahaddatan Kur'ani da Kyautar Miliyoyin Naira
- Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bai wa ɗalibai 30 da suka kammala haddar Alƙur’ani a Cibiyar Musulunci kyautar miliyoyin Naira
- Daliban sun haddace Alƙur’ani mai girma ne ƙarƙashin tallafin fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Muhammadu Indimi a jihar Borno
- Zulum ya kuma bai wa malamai takwas da suka koyar da ɗaliban Naira miliyan biyu kowanne, tare da yin kira ga malaman addini da su yi wa’azi cikin tawali’u
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Maiduguri – Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bai wa ɗalibai 30 da suka kammala haddar Alƙur’ani mai girma kyautar Naira miliyan 1 kowanne.
An gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a Masallacin Indimi da ke tsohuwar hanyar Damboa a Maiduguri, inda aka karrama ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani gaba ɗaya ƙarƙashin tallafin Alhaji Muhammadu Indimi.

Source: Facebook
Miliyoyin da Zulum ya bayar
A sakon da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya ya wallafa a Facebbok, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin ba da Naira miliyan 30 ga ɗalibai 30, wato Naira miliyan ɗaya ga kowanne.
Ya kuma bayar da umarnin bai wa malamai takwas da suka koyar da ɗaliban Naira miliyan biyu kowanne, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 16.
Rahoto ya nuna cewa jimillar kuɗin da gwamnan ya bayar ga ɗalibai da malaman ta kai Naira miliyan 46.
Zulum ya yabawa Indimi
Da yake jawabi a wajen bikin, Zulum ya yabawa Alhaji Muhammadu Indimi bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimin addinin Musulunci da haɓaka ƙwarewar al’umma.
Indimi, wanda shi ne wanda ya kafa kuma shugaban kamfanin Oriental Energy Resources, ya daɗe yana tallafawa harkar ilimi a Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya.
Gidauniyar tasa ta taimaka wajen tallafawa harkokin ilimi, ciki har da gudunmawar Naira biliyan biyu da ta bayar kwanan nan ga asusun tallafawa ilimi na Jami’ar Maiduguri.
Kiran Zulum ga malamai
Gwamna Zulum ya buƙaci malaman addini da su riƙa yin wa’azi cikin tawali’u da natsuwa, tare da guje wa kalamai da za su iya haddasa rikici ko rarrabuwar kawuna.
Ya ce ya kamata malamai su mayar da hankali kan koyarwar da ke ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da kishin ƙasa tsakanin Musulmi.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafawa ilimin zamani da na addini, yana mai cewa haɗa ilimin Musulunci da na zamani na da matuƙar muhimmanci.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elakanemi; Sanata Mohammed Tahir Monguno da sauransu.
Kirista ya ci kyautar Umrah
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani Kirista a Masar mai suna Mina ya lashe kyautar Umrah bayan ya shiga wata gasar addinin Musulunci da ake gwada ilimin Alƙur’ani.
Mina ya shiga gasar ne ba domin ya je Umrah da kansa ba, sai dai domin ya bai wa maƙwabciyarsa Musulma, Um Ali ko Mona, damar zuwa aikin Umrah.
Rahotanni sun ce Mina ya ga Mona tana shiga gasar a wani shirin kai tsaye na kafafen sada zumunta, inda ya yanke shawarar shiga domin ya taimaka mata.
Asali: Legit.ng

