Magana Ta Fito: An Bayyana Wadda Ta Yi Silar Hadakar Obi da Kwankwaso
- KNN ta warware biri har wutsiya kan yadda aka kulla hadakar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
- Kungiyar ta ce tattaunawar ta taimaka wajen zaburar da shirin kafa kawancen siyasa tsakanin Arewa da Kudu gabanin zaben 2027
- KNN ta yi alkawarin tattara kuri’u miliyan biyar daga Kudu maso Gabas domin goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Umuahia, Abia - Jagoran kungiyar Kwankwaso National Network (KNN) a shiyyar Kudu maso Gabas, Dr Ukpai Iro Ukpai, ya bayyana yadda wata magana daga Dr Aisha Rabiu Kwankwaso ta zaburar da kokarin hada mahaifinta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Peter Obi.
Ukpai ya ce tattaunawar ta gudana ne a gidan Kwankwaso, inda Aisha ta tambayi mahaifinta dalilin da ya sa ba zai yi aiki tare da Obi ba.

Source: Facebook
Ukpai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard a birnin Umuahia na jihar Abia.
Ya ambato ta tana cewa:
“Daddy, me ya sa ba za ka tafi tare da wannan mutumin Obi ba?”
A cewar Ukpai, tambayar ta sa Kwankwaso yin la’akari da wata babbar hadaka ta kasa maimakon mayar da hankali kan bambancin yanki da burin siyasa.
KNN ta yaba wa Aisha Kwankwaso
Ukpai ya ce ya kamata a bai wa Aisha yabo da karramawa saboda rawar da ta taka wajen zaburar da wannan tunanin.
Ya bayyana Aisha, wadda sabuwar likita ce da ta kammala karatu, a matsayin wakiliyar matasa da kuma hadin kan kasa.
A cewarsa, ta ga yiwuwar hada hangen Obi kan tattalin arziki da kuma karfin Kwankwaso na samun goyon bayan jama’a a matakin kasa.
Ukpai ya ce tambayar Aisha ta nuna yadda matasan Najeriya ke kara neman shugabannin da za su hada kan al’umma ba tare da la’akari da bambancin kabila ko yanki ba.
Ana neman gina kawancen Arewa da Kudu
Jagoran na KNN a Kudu maso Gabas ya ce bayan wannan tattaunawa, kokarin gina kawancen siyasa tsakanin Arewa da Kudu ya kara samun karfi.
Ya ce kungiyar KNN ta shiyyar Kudu maso Gabas ta amince da Aisha a matsayin memba na girmamawa saboda rawar da ta taka wajen zaburar da shirin hadin kan siyasa.
Ukpai ya ce kawancen Obi da Kwankwaso, idan aka kammala shi, zai iya zama babban karfi a zaben shugaban kasa na 2027.
KNN na neman kuri’u miliyan 5
Ukpai ya bayyana Kwankwaso a matsayin “mai mutane”, yana mai kwatanta tsarin siyasarsa da na marigayi dattijo Maitama Sule da marigayi Malam Aminu Kano.
A cewarsa, karfin Kwankwaso a Arewa da kuma goyon bayan Obi a Kudu, musamman tsakanin matasa, na iya samar da tubalin wata babbar kawancen kasa.
Ya ce KNN za ta ci gaba da tattara goyon baya a Kudu maso Gabas da sauran sassan Najeriya domin tabbatar da tsarin siyasar da take ganin zai karfafa hadin kan kasa.
Ukpai ya ce kungiyar ta kuduri aniyar tattara kuri’u miliyan biyar daga Kudu maso Gabas domin goyon bayan tikitin hadin gwiwar Obi da Kwankwaso a zaben 2027.
Ya kara da cewa yakamata sauye-sauyen siyasar da ake samu gabanin zaben su dogara kan kwarewa, hadin kai da kuma kudurin magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke addabar Najeriya.

Source: Facebook
Dickson ya gana da Kwankwaso, Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar NDC, Sanata Henry Seriake Dickson, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su haɗa kai domin tabbatar da nasarar 'yan takararta a zaben 2027.
Sanata Dickson ya yi kiran ne bayan tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, da wanda zai masa mataimaki, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Legit.ng


