Wata Sabuwa: Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso Ta Zargi INEC da Sauya Sunayen 'Yan Takararta
- Jam’iyyar NDC ta zargi INEC da maye gurbin wasu ‘yan takararta da sunayen mutanen da ba ta zaɓa ko miƙa wa hukumar ba
- Shugaban NDC, Moses Cleopas, ya ce an samu matsalar musamman a Anambra, inda aka wallafa sunaye tara da jam’iyyar ba ta sani ba
- Jam’iyyar ta buƙaci INEC ta gudanar da bincike tare da dawo da sunayen ‘yan takarar da ta tantance, tana shirin ɗaukar matakin shari’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Yaƙin neman zaɓen 2027 ya ɗauki sabon salo bayan jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wallafa sunayen ‘yan takarar da ba ta tsayar ba.
Jam’iyyar NDC ta yi zargin cewa hukumar ta maye gurbin wasu daga cikin ‘yan takarar da ta tantance da wasu sunaye da ba a san su ba.

Source: Facebook
NDC ta ce an wallafa sunaye tara a Anambra
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, ya bayyana zargin ne cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar Leadership.
Cleopas ya ce INEC ta saka wasu sunaye a matsayin ‘yan takarar NDC a zaɓen ‘yan majalisar dokokin jihar Anambra, duk da cewa jam’iyyar ba ta tsayar da su ba.
Ya ce sunayen da ake takaddama a kansu sun haɗa da Umennaajiego Jude Ezenwa na Onitsha South; Akpotue Obinna Chibuike na Onitsha South 2; Nwankwo Chiemerie na Orumba North; da Maduagwu Eric na Anaocha 1.
Sauran sunayen sun haɗa da Ngoebisi Obinna na Idemili North; Isintume Charles na Njikoka 1; Nwachukwu Nonso na Nnewi South 1; Okeke Ifeanyi Akunne na Nnewi South 2; Nnonyelu Samson E na Ayamelum da Azotani Chuks Francis na Dunukofia.
Cleopas ya bayyana yadda matsalar ta faru
Shugaban NDC ya ce shi ne ke riƙe da lambar da INEC ta bai wa jam’iyyar domin loda sunayen ‘yan takararta, amma bai loda sunayen da aka wallafa ba.
Ya bayyana cewa bayan kammala zaɓen fidda gwani da sauraron ƙorafe-ƙorafe, shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki sun samar da jerin sunayen ƙarshe tare da sanya hannu a kansu.
A cewarsa, lokacin da aka loda jerin sunayen zuwa shafin INEC, jami’an hukumar da ke kula da tsarin suka bar sunaye tara cikin matsayin “jira”, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Cleopas ya ce daga baya INEC ta bayyana cewa sunayen sun riga sun kasance cikin tsarin hukumar, saboda jami’an da suka sa ido kan zaɓen fidda gwani na NDC ne suka gabatar da su.
Ya ce jam’iyyar ta ƙalubalanci sunayen tare da miƙa wa INEC sunayen ‘yan takarar da ta amince da su, amma hukumar ta ƙi sauya su.
Shugaban NDC ya ce binciken farko da jam’iyyar ta gudanar ya nuna yiwuwar wasu jami’an INEC suna da hannu wajen sauya sunayen. Ya kuma yi zargin cewa makamancin matsalar ta faru a wasu mazabu a Benue da Imo.
NDC ta buƙaci INEC ta gudanar da bincike
Cleopas ya buƙaci shugaban INEC da ya fara bincike cikin gaggawa domin gano yadda sunayen da jam’iyyar ba ta amince da su suka shiga cikin jerin ‘yan takarar da aka wallafa.
Ya ce jam’iyyar na ganin abin da ya faru a matsayin yunƙurin kunyata ta, tsoratar da magoya bayanta da kuma haifar da rarrabuwa a cikinta.
Cleopas ya kuma zargi INEC da hana wasu jam’iyyun siyasa, musamman na adawa, loda halastattun ‘yan takararsu yayin da ake zargin ana tilasta musu wasu sunaye.
NDC ta shirya zuwa kotu
Jam’iyyar ta ce ba za ta tsaya kan lamarin ba, inda za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da cewa an dawo da sunayen ‘yan takarar da ta tantance.
Cleopas ya bayyana cewa NDC na shirin garzayawa kotun da ke da hurumin sauraron ƙarar domin neman a gyara abin da ta bayyana a matsayin kuskure da kuma dawo da sahihan ‘yan takararta.

Source: Facebook
Tanadin NDC kan nada mukamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana shirin jam’iyyar kan nada mukamai idan ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kwankwaso ya ce ta karewa su Ganduje a Kano Ya bayyana cewa za a rika yin naɗe-naɗen mukaman siyasa ne bisa cancanta da kuma bukatun ƙasar ba wai wasu dalilai na kusanci ba.
Asali: Legit.ng



