Shawarar da Jamilu Zarewa Ya Ba 'Yanuwansa Malamai kan goyon bayan Muslim Muslim

Shawarar da Jamilu Zarewa Ya Ba 'Yanuwansa Malamai kan goyon bayan Muslim Muslim

  • Jamilu Yusuf Zarewa ya tuna wa malamai bukatar jin tsoron Allah SWT wajen tallata ‘yan takara ko gwamnati
  • Malamin musuluncin da yake koyarwa jami’ar ABU Zaria bai sukar shigar malamai cikin siyasa a Najeriya
  • Sheikh Zarewa yana so ko malami zai yi takara, ya zama ya cancanta kuma yana ganin zai iya kawo sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Jamilu Yusuf Zarewa wanda malamin addini ne, ya shiga cikin maganar goyon bayan ‘yan siyasa da wasu suke yi.

An samu malaman Musulunci suna fitowa cikin bainar jama’a, suna bayyana goyon bayansu ga wasu ‘yan siyasa gabanin zabe.

Tinubu
Bola Tinubu a UAE da hoton Sheikh Jamilu Zarewa yana karatu Hoto: Getty Imges/Jamilu Zarewa
Source: AFP

Jamilu Yusuf Zarewa ya tabo batun Muslim-Muslim

Associate Professor Jamilu Yusuf Zarewa ya yi rubutu a Facebook wanda ya yi take da suna tikitin Musulmi da Musulmi - Nasihata.

Malamin na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya fara da yin nasiha da ‘yanuwansa malamai da dalibai su yi hattara da kimarsu.

Kara karanta wannan

'Matsala ne dawo da tallafin mai': Malamin Musulunci ya gargaɗi ƴan siyasa kan kamfe

A ra’ayin malamin wanda babban masanin ilmin Usulul fikihu ne, tikitin Musulmi da Musulmi dabarar siyasa ce ba wai kishin addini ba.

Jamilu Zarewa ya yi kira ga magada Annabawa su sa tsoron Ubangiji SWT idan har za su fada wa mutane su zabi gwamnati mai-ci.

Sheikh Zarewa bai hana malamai siyasa ba

Shehin bai ganin cewa laifi ne malaman addini su shiga siyasa, ya ce duk wanda ya yarda da cancantarsa zai iya fitowa neman takara.

Sai dai muddin malami ya shiga siyasa, Sheikh Zarewa ya ce idan aka ci masa mutunci ba zai yiwu a ce an taba addinin musulunci ba.

Duk da ya ga dacewar shehin da ya cancanta ya shiga siyasa, yana ganin zai fi kyau malamai su tsaida hannun wani cikin almajiransu.

Ya bude kofa malami ya tsunduma irin wannan siyasa ta Najeriya ne idan zai iya kawo gyara ko yana da kyakkyawan zaton hakan.

Nasihar Jamilu Yusuf Zarewa a Facebook

MUSLIM - MUSLIM TICKETS - NASIHATA
- Daga Asc. Professor Jamilu Zarewa

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

1. Ya kamata malamai da Daliban ilimi su kiyaye mutuncinsu.
2. Muslim - Muslim ba shi da alaka da addini, siyasa ce kawai da kuma lissafin yadda za a ci zabe.
3. Duk Wanda zai tallata wannan Gwamnatin ya ji tsoron Allah, kuma ya san zai maimata abin da ya fada.
4. Kusukure ne idan aka zagii malamin da ya zunduma kansa a SIYASA ace an taba sddini saboda Neman Duniya ya je.
5. Duk malamin da aka ba shi kudi saboda da tasirinsa , ya wajaba ya samma dalibansa.
6. Siyasar Nigeria Kazama ce, ya kamata magada Annabawa su yi ta da takatsantsan.
7. Babu laifi Malami ya shiga SIYASA in ya yarda da Capacity nasa..
8. Inda yanayi yana jin wa'azinmu akan WADATAR ZUCI da ba a samu ruwan koramar da zai gangara cikin kogi ba.
9. Babu laifi malami ya zunduma cikin siyasa in ya gamsu zai kawo gyara ko kuma mafi rinjayan zato.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

10. Abin da ya fi kamata ga Malamin addini shi ne ya zama uba, in ya samu Mai dama-dama a cikin dalibansa ko wadanda ya sani ya dafa musu.

- JYZ

Kwamitin yakin zaben Tinubu ya sha suka

An ji cewa ‘yan majalisar tarayya daga APC, ADC da NDC sun soki haɗa jami’an gwamnati da ‘yan siyasa a kwamitin yakin zaben Bola Tinubu.

Sun nuna fargabar cewa saka Shugaban Hukumar Haraji a kwamitin nemo wa APC kudi zai iya haifar da zargin amfani da kudin haraji cikin kamfe.

'Yan majalisar sun kuma yi tir da nada ministocin tsaro da shugaban ofishin kasafin kudi, Tanimu Yakubu a matsayin ma'aji na kwamitin yakin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng