Iran Ta Kara kai Hare Hare kan Amurka, Ta Yi Ruwan Wuta a UAE
- Rundunar sojin Iran ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da jirage marasa matuka masu ɗauke da abubuwan fashewa
- Iran ta ce harin ramuwar gayya ne kan wani hari da Amurka ta kai wa tsibirin Larak a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwa tare da jikkata wasu mutane
- Rundunar sojin Iran ta kuma yi barazanar ci gaba da kai hare-hare kan sojojin Amurka, yayin da manyan kwamandojin sojin Amurka suka gargadi Pete Hegseth
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Iran ta ce ta kai wani hari kan sojojin Amurka da jirage masu saukar ungulu da ke sansanin Al Minhad a Hadaddiyar Daular Larabawa da jirage marasa matuka masu ɗauke da abubuwan fashewa.
Rundunar sojin Iran ta bayyana cewa matakin ya kasance ramuwar gayya ne kan harin da sojojin Amurka suka kai wa tsibirin Larak da ke Iran ranar Lahadi.

Source: Facebook
An kai hari sansanin Amurka
Anadolu ya rahoto cewa rundunar sojin Iran ta ce ta kai hari kan wuraren da ke ɗauke da sojojin Amurka da jiragen yaƙi masu saukar ungulu a sansanin Al Minhad da ke UAE.
Rundunar ta ce an kai hare-haren ne da dama daga cikin jirage marasa matuki masu ɗauke da abubuwan fashewa, inda ta bayyana sansanin a matsayin muhimmiyar cibiyar jigilar kayayyaki da sojoji ta sama ga dakarun ƙasashen waje.
Bayan kai farmakin, Iran ta kuma yi alkawarin ɗaukar wasu matakai kan sojojin Amurka a matsayin ci gaba da ramuwar gayya.
Dalilin Iran na kai hari UAE
Rundunar sojin Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan kisan wasu mambobin Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) da fararen hula a wani hari da Amurka ta kai wa tsibirin Larak ranar Lahadi.
A ranar Lahadin ne sojojin Amurka suka kai hari kan wasu na’urorin harba makamai masu linzami guda biyu a tsibirin Larak, lamarin da ya zama hari na farko da Amurka ta kai kan ƙasar Iran tun ƙarshen watan Yuli.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta hango matsala, Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a wasu wurare
Amurka ta ce an kai harin ne kan na’urorin da ake zargin ana shirin amfani da su wajen harba rokoki masu ɗauke da nakiyoyi zuwa mashigin ruwan Hormuz.
Korafin kwamandojin Amurka
A gefe guda, wasu manyan jami’an sojin Amurka sun gargadi Ministan Tsaro, Pete Hegseth, kan ci gaba da gudanar da manyan hare-hare a Iran.
Al Jazeera ta rahoto cewa shugabannin rundunonin sojin ƙasa, ruwa da sama na Amurka, da kuma kwamandojin sojojin Amurka da ke Turai, Asiya da Latin Amurka, sun nuna damuwa kan ci gaba da yaƙin.

Source: Getty Images
Abin da ya faru a Larak
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran da Amurka sun yi musayar hare-hare bayan da sojojin Amurka suka kai hari kan wasu na’urorin harba rokoki guda biyu a tsibirin Larak da ke mashigar ruwan Hormuz.
Harin Amurkan, wanda shi ne na farko da aka tabbatar tun ƙarshen watan Yuli, ya kashe mutane biyu tare da jikkata wasu biyu, a cewar Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran.
Amurka ta ce ta ɗauki matakin ne cikin iyaka kuma daidai, domin dakile sojojin Iran da ake zargin suna shirya shimfiɗa nakiyoyi a mashigin ruwan Hormuz, ind Iran ta mayar da martani.
Asali: Legit.ng
