Gwamnoni 3 Sun Zauna a Gida, ba Su Halarci Tantancewar APC gabanin Zaben 2027 ba
- Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa gwamnoni uku ba su samu halartar tantancewar shirin tunkarar babban zaben 2027
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda ya ce gwamnonin sun bada uzuri kuma za a tantance su a duk lokacin da suka shirya
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Katsina, Malam Dikkko Radda na cikin wadanda aka tantance zuwa yanzu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnonin jam'iyyar APC uku ba su samu damar halartar wurin tantancewar da aka gudanar yau Asabar, 10 ga watan Mayu, 2026.
Kwamitin tantancewa da APC ta kafa karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fara tantance gwamnonin a wani bangare na shirin 2027.

Source: Twitter
Sai dai, rahoton da The Cable ta wallafa yau Asabar ya nuna cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara; gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru; da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ba su halarci tantancewar ba.

Kara karanta wannan
Pantami ya bayyana muhimmancin zaben fitar da gwani ga jam'iyyar APC, ya yi gargadi
Me yasa gwamnoni 3 ba su halarta ba?
Da yake magana yayin gudanar da aikin, Shugaban APC, Farfesa Yilwatda ya ce gwamnonin uku sun nemi afuwa ne saboda wasu harkokin gwamnati da suka taso a jihohinsu.
“Gwamnonin uku da ba su bayyana ba, duk sun bayar da dalilan rashin zuwansu,” in ji shi.
Ya kara da cewa kasancewarsu shugabannin zartarwa na jihohinsu ya sa aka ba su damar zuwa a lokacin da suka samu dama.
“Gwamnan Kwara ya ce yana da harkokin gwamnati, mun ba shi uzuri. Gwamnan Ebonyi ma haka, haka kuma gwamnan Rivers,” in ji shugaban APC.
Yaushe APC za ta tantance gwamnonin?
Yilwatda ya bayyana cewa APC za ta ci gaba da tantance gwamnonin duk lokacin da suka samu damar halarta.
“Mun ce su shugabanni ne kuma kwamandoji a jihohinsu. Duk lokacin da suka samu dama su kira kwamitin tantancewa, za mu ba su wuri su zo a lokacin da ya dace da su,” in ji shi.
Gwamnonin da suka halarta
Daga cikin gwamnonin da aka tantance akwai Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, Nasir Idris na Kebbi, Caleb Mutfwang na Plateau da Hyacinth Alia na Benue.
Sauran sun hada da Sheriff Oborevwori na Delta, Umar Bago na Neja, Dauda Lawal na Zamfara, Bassey Otu na Cross River da Ahmed Aliyu na Sokoto.

Source: Twitter
Wannan tantancewa wani bangare ne na shirye-shiryen da APC ke yi domin tunkarar babban zaben 2027.
Jam'iyyar ta fara tattaunawa da tantancewa ta cikin gida musamman gwamnonin da ke kan mulki da kuma manyan masu ruwa da tsaki domin gane irin karfin da take da shi kafin 2027, in ji rahoton Guardian.
APC ta tara fiye da Naira biliyan 4
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC ta samu sama da Naira biliyan 4.45 daga sayar da fam ga wadanda ke neman takarar kujerar gwamna a 2027.
Bayanai sun nuna cewa APC ta samu Naira miliyan 200 daga Shugaba Bola Tinubu da Stanley Osifo, waɗanda suka sayi fam.ɗin neman takarar shugaban ƙasa.
Haka kuma, APC ta sayar da fam ɗin gwamna kan Naira miliyan 50, na.Sanata kan Naira miliyan 20, yayin da na ɗan majalisar wakilai ya kai Naira miliyan 10.
Asali: Legit.ng

