APC Ta Tara N4.4bn daga Sayar da Fam na Takarar 2027 duk da Rikicin Jam'iyya
- Jam’iyyar APC ta samu sama da Naira biliyan 4.45 daga sayar da fam ga wadanda ke neman takarar kujerar gwamna a 2027
- Ta yi wannan ciniki ne duk da rikicin da ya ɓarke a cikin ƙungiyar gwamnonin APC yayin da gwamnoni 18 suka bi bayan ga Hope Uzodinma
- Tuni jam'iyyar APC ta fara tantance masu neman takarar gwamnoni da ‘yan majalisu kafin zaɓen fitar da gwani da za a yi nan gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Yayin da jam’iyyun adawa ke fama da rarrabuwar kai gabanin babban zaɓen shekarar 2027, APC mai mulki ta ƙara ƙarfafa matsayinta na siyasa.
Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzu ta tara sama da Naira biliyan 4.45 daga sayar da fam ɗin nuna sha’awar tsaya wa takara.

Source: Facebook
Arise News ta kawo rahoton cewa APC ta samu wannan kuɗi ne daga masu neman takarar shugaban ƙasa biyu.
Sai kuma masu neman takarar gwamnoni 83 daga jihohi 28, tare da masu neman kujerun majalisun tarayya da na jihohi.
Jam'iyyar APC ta tara kudin fam
Bayanai daga jaridar This day na cewa APC ta samu Naira miliyan 200 daga Shugaba Bola Tinubu da Stanley Osifo, waɗanda suka sayi fam ɗin neman takarar shugaban ƙasa.
Haka kuma, an sayar da fam ɗin gwamna kan Naira miliyan 50, na Sanata kan Naira miliyan 20, yayin da na ɗan majalisar wakilai ya kai Naira miliyan 10.
Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da ake zargin rikici ya ƙara tsananta a cikin ƙungiyar gwamnoni ta PGF.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya samu goyon bayan gwamnoni 18 daga cikin gwamnoni 31 na APC bayan wata ganawar sirri da suka yi a Abuja.
Rikici ya tarnake gwamnonin APC
Tun farko dai an ruwaito cewa wasu gwamnoni sun yi yunƙurin cire Uzodinma daga shugabancin ƙungiyar tare da maye gurbinsa da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah.

Source: Facebook
Rahotanni sun kuma nuna cewa wata ƙungiya a cikin PGF na ƙarƙashin jagorancin gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da takwaransa na Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.
Bayan taron da suka gudanar a Abuja, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa babu wata matsala a cikin ƙungiyar.
Shi ma gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce rahotannin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne, babu wata matsala a kungiyar.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da na jihar Kano, Ondo, Kaduna, Sakkwato, Ebonyi, Borno, Legas, Kebbi da Binuwai, yayin da wasu jihohi suka samu wakilcin mataimakan gwamnoni.
Rikici ya barke tsakanin gwamnonin APC
A baya, mun kawo labarin cewa wani babban rikicin shugabanci ya ɓalle a cikin ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF), inda gwamnonin suka dare zuwa gida biyu.
Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya nace cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban PGF, kuma Uba Sani na Kaduna ne mataimakinsa duk da rigimar da ta taso.
Wani ɓangaren gwamnonin kuma sun kafa tasu ƙungiyar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dapo Abiodun da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq suna kalubalantar su Uzodinma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


