Kallo Ya Koma Sama Yayin da APC Ta Tantance Gwamnoni 14 Babu Sunan Fubara

Kallo Ya Koma Sama Yayin da APC Ta Tantance Gwamnoni 14 Babu Sunan Fubara

  • Jam'iyyar APC na ci gaba da tantance gwamnoni masu neman zarcewa da kuma wadanda ke neman kujerun sanatoci a Najeriya
  • Akalla yanzu an tantance gwamnoni 14 amma babu sunan Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara inda ka ace bai halarci tantancewar ba
  • APC ta fara gudanar da tantancewar ‘yan takara gabanin zaben fidda gwani, yayin da Stanley Osifo ya zama mutum tilo da ya kalubalanci Bola Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar APC ta fara tantance masu neman takara gabanin babban zaben shekarar 2027, inda aka tantance gwamnoni 14.

Daga cikinsu akwai masu neman zarcewa da sauran masu neman mukaman siyasa daban-daban.

An rasa sunan Fubara cikin wadanda APC ta tantance
Gwamna Siminalayi Fubara yayin jawabi ga al'ummar Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Sai dai gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, bai bayyana a wajen tantancewar ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasar jihar, cewar Punch.

APC ta fara tantance yan takara a Abuja

Kara karanta wannan

APC ta tara N4.4bn daga sayar da fam na takarar 2027 duk da rikicin jam'iyya

Rahotanni sun nuna cewa APC ta fara sayar da fom din nuna sha’awa da takara tun ranar 28 ga Afrilu, yayin da aka rufe sayarwar a ranar 6 ga Mayu.

An fara tantance gwamnoni masu ci tun ranar 8 ga Mayu, yayin da ake sa ran kammala aikin a ranar Lahadi.

Daga cikin gwamnoni da aka tantance akwai Abba Yusuf na Kano, Inuwa Yahaya na Gombe, Nasir Idris na Kebbi, Caleb Muftwang na Plateau da Hyacinth Alia na Benue.

Sauran sun hada da Francis Nwifuru na Ebonyi, Sheriff Oborevwori na Delta, Umar Bago na Neja, Dauda Lawal na Zamfara da Ahmed Aliyu na Sokoto.

A bangaren takarar shugaban kasa, Stanley Osifo ne kadai ya fito domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben fitar da gwani na APC.

Osifo ya bayyana cewa an yi masa tambayoyi masu tsauri yayin tantancewar, ciki har da dalilin da ya sa yake son fafatawa da shugaban kasa mai ci.

Ya ce duk da goyon bayan da shugabannin jam’iyyar suka bai wa Tinubu, har yanzu yana nan daram a takararsa kuma bai taba tunanin janyewa ba.

Kara karanta wannan

An saka sunan El Rufai, Ganduje da Malami kan zargin kisan Dadiyata

APC za ta kammala tantance gwamnoni a yau
Shugaban APC a Najeriya, Nentawe Yitwalda. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Gwamnonin da ba su halarci tantancewar ba

Shugaban kwamitin tantancewar APC, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa gwamnoni uku ne ba su halarci tantancewar ba saboda wasu ayyukan gwamnati da suka taso musu.

Ya ce duk gwamnan da ke da uzuri zai samu wata dama cikin wa’adin da aka tsara domin tantancewar, cewar TVC News.

A Rivers kuwa, rahotanni sun nuna cewa wasu manyan ‘yan siyasa ne suka sayi fom din takarar gwamna wa Sim Fubara ta hanyar wakilai duk da rikicinsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Haka kuma, an ce dan majalisar wakilai Kingsley Chinda da tsohon kwamishina Das George-Kelly sun sayi fom din takarar gwamna a karkashin APC a Rivers.

Wike ya musanta tsayar da dan takara

An ji cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi karin haske game da batun fitar da dan takara ko goyon bayansa a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Sunaye: APC Ta tantance gwamnoni 12, ta amince su nemi tazarce a babban zaben 2027

Wike ya ce bai goyi bayan kowa domin takarar gwamnan Rivers ta 2027 ba, yana jiran hadakar PDP da APC ta yanke matsaya.

Ya bayyana cewa ba su aiki tare da Gwamna Siminalayi Fubara, har yana zarginsa da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.