Delta
Duk da dokar dake haramta mu'amala tsakanin jinsi daya a Najeriya, Google ta bayyana cewa akwai yuwuwar cigaba da mu'amalar jinsi tare da hauhawa a Najeriya...
Karshen tika tika tik! Biyo bayan doguwar tirka tirka a gaban kotuna daban daban, daga karshe kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da gwamnonin jahohin Neja, Delta da Abia suka samu a yayin zaben gwamnoni na shekarar 2019.
Gungun yan bindiga dake fashi a kan teku sun halaka zaratan dakarun rundunar Sojin ruwan Najeriya guda hudu daga cikin Sojoji shida da suka kai agajin gaggawa ga wani babban jirgin ruwa da yan bindigan suka tare.
Wani magidanci ya hau dokin zuciya inda ya yi amfani da adda wajen sassara mahafiyar uwargidarsa a gidanta dake titin Arubayi cikin garin Warri na jahar Delta, daga bisani kuma ya kwankwadi gubar da ta kashe shi.
Mutanen garin Asaba, cikin jihar Delta har yanzu ba su gama jimamin yadda wani saurayi dan shekara 19 ya dirkawa mahaifiyar shi cikin shege ba, a yayin da yake gwaji na abubuwan surkullen shi...
Ministan fetur Timipre Sylva ya ce za su ba Matatar Dangote goyon baya inda ya ce za su taimakawa matatar Dangote tare da dafawa Dangote da danyen man fetur domin ya yi nasara.
Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Litinin, 14 ya watan Oktoba, sun kai farmaki a yankin Issele-Azagba kusa da Asaba, jihar Delta sannan suka sace yara biyu daga wata makarantar kudi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ovie Omo-Agege, ya yabawa mutanen Delta ta tsakiya bayan ya yi nasara a kotu. Omo Agege ya ji dadin tika ‘Yar takarar Jam’iyyar PDP da kasa a zaben na bana.
Wani bidiyo da ya fara yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo ya nuna yadda wani dan damfara na yanar gizo wanda aka fi sani da 'Yahoo Boy', mai suna Junior ya haukace bayan ya kasa kai mahaifiyarsa ayi asiri da ita a jihar...
Delta
Samu kari