Yadda Tinubu da Abokinsa Suka Kusa Fadawa Gadar Legas a Hadarin Mota
- Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kuma ɗan jarida, Sanata Babafemi Ojudu, ya bayyana yadda shi da Shugaba BolaTinubu suka tsallake wani hatsarin mota
- Ojudu ya ce lamarin ya faru ne jim kaɗan kafin Tinubu ya zama gwamnan jihar Legas, lokacin da direbansu ya yi barci a kan hanya
- Ya bayyana cewa ya tuna da lamarin ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Tinubu, inda ya kuma buƙaci shugaban ya sake duba wasu manufofin gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara, Sanata Babafemi Ojudu, ya bayyana yadda shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka tsallake wani hatsarin mota a gadar Third Mainland da ke Legas.
Ojudu ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa ta musamman da ya rubuta wa Tinubu domin tunawa da ranar samun ’yancin kan Najeriya, inda ya yi amfani da labarin wajen bayyana irin tsawon dangantakar da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya bukaci Atiku da Peter Obi su janyewa Tinubu, ya kawo hujja

Source: Facebook
Yadda hatsarin ya faru
Daily Trust ta wallafa cewa Ojudu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, lokacin da shi da Tinubu ke dawowa daga gidan wani babban jami'in tsaro mai suna Ibrahim Solomon a Ikoyi.
Ya ce direban Tinubu, marigayi Mustapha, ya yi barci yayin da yake tuƙi a kan gadar Third Mainland, lamarin da ya sa motar ta bugu da katangar gadar.
Ojudu ya ce duk da hatsarin, shi da Tinubu sun tsira da rayukansu.
Ya ce:
“A kan hanyarmu ta dawowa, da misalin ƙarfe 1:30 na dare, direbanka marigayi Mustapha ya yi barci yana tuƙi a kan gadar Third Mainland. Motar ta bugu da katangar gadar. Mun yi sa'a da muka tsira da rayukanmu.”
Tinubu ya nemi Ojudu ya tuƙa motar
Ojudu ya ƙara da cewa bayan hatsarin, Tinubu ya roƙe shi ya tuƙa motar zuwa Alausa, duk da cewa bai taɓa tuƙin mota irin ta ba.
Ojudu ya ce ya tuna da wannan lamari ne saboda yana nuna irin tsawon dangantakar da ke tsakaninsa da Tinubu, wadda ta samo asali tun lokacin gwagwarmayar da suka yi da mulkin soja da kuma kamfen ɗin Tinubu na neman zama gwamnan Legas.

Source: Getty Images
Bayan Tinubu ya lashe zaɓen gwamna, Ojudu ya ce ya taimaka wajen tafiyar da kwamitocin mika mulki da shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnati.
Sai dai ya ce ya ƙi karɓar wani matsayi a gwamnatin, inda ya koma aikin jarida saboda yana ganin Tinubu na buƙatar mutum a wajen gwamnati da zai riƙa gaya masa gaskiya ba tare da neman wata alfarma ko matsayi ba.
Dangantakar Ojudu da Tinubu
Ojudu ya ce a lokacin da Tinubu ke gwamnan Legas, ya yi ƙoƙarin taka wannan rawa, ba tare da zuwa wurinsa neman mukami ko wata alfarma ba.
Ya ce tsohon shugaban ma’aikatan Tinubu, Alhaji Lai Mohammed, kan yi masa wasa idan ya gan shi a ofishin gwamnan, yana cewa:
“Abokin hamayyarmu ya zo. Me muka sake yi ba daidai ba?”
Ojudu ya ce a irin wannan yanayi ne ya rubuta wasiƙar ga Tinubu duk da cewa dangantakarsu ta yi tsami a shekarun baya.

Kara karanta wannan
Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai
Ya bayyana cewa shi da Tinubu ba su sake haɗuwa tun daga shekarar 2022 ba, sannan ya bayyana a fili cewa bai yi wa Tinubu aiki a kamfen ɗin shugaban ƙasa na 2023 ba kuma bai zaɓe shi ba.
Malamai na adawa da Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu malaman addinin Musulunci sun gudanar da wani taro a jihar Kano domin bayyana matsayinsu kan neman tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa malaman sun gudanar da taron ne bayan sun ce sun yi nazari kan yadda Tinubu ya tafiyar da Najeriya tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Matakin malaman ya zo ne a daidai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki ke gudanar da ƙoƙarin neman goyon bayan malamai da sauran masu tasiri a cikin al'umma gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng
