Gwamnatin Uba Sani Ta Fadi Abu 2 da Suka Fi Rashin Tsaro Barazana ga Zaman Lafiya
- Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya ce labaran ƙarya na iya ƙara tayar da hankali da rashin yarda a tsakanin jama’a
- Gwamnatin Kaduna ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da NIPR wajen inganta sadarwa da tallata al’adu da damar zuba jari a jihar
- NIPR ta ce hulɗar jama’a ba sana’a kawai ba ce, tana kuma taimakawa wajen gina amana, bunƙasa ƙasa da samar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su da tushe a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya fiye da rashin tsaro.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2026 yayin da ya karɓi shugabannin reshen Kaduna na Nigerian Institute of Public Relations (NIPR).

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce shugabannin sun kai wa kwamishinan ziyara ne a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen wayar da kan jama’a gabanin taron ƙasa da ƙasa na NIPR na 2026 da za a gudanar a Abuja.
Labaran ƙarya na iya ƙara tayar da hankali
Maiyaki ya ce yaɗa bayanan ƙarya na da ƙarfin tayar da hankali, ƙara rashin yarda tsakanin jama’a da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Kaduna da sauran sassan Najeriya.
“Ina ganin wajen tallata Kaduna yadda ya kamata, maimakon ba da rahoton saɓani, ya kamata mu fahimci cewa rashin tsaro ba barazana ce ga zaman lafiya kawai ba, labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su da tushe sun fi zama babbar barazana,” in ji shi.
Kaduna za ta tallata damar zuba jari
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wajen yin aiki tare da ƙungiyoyin ƙwararru, ciki har da NIPR, domin inganta sadarwa, ƙarfafa amincewar jama’a da kuma kyautata matsayin Kaduna.
Ya ce taron NIPR zai bai wa Kaduna damar nuna al’adunta, damar zuba jari da sauran nasarorin jihar ga mutane daga sassa daban-daban.
A cewarsa, Kaduna za ta shiga baje kolin da za a gudanar yayin taron domin nuna al’adunta da damar zuba jari, musamman a fannin haƙar ma’adanai da sauran sassa.
Gwamnati ta ce an samu ƙarin jari
Maiyaki ya ce jihar ta samu gagarumar shigowar masu zuba jari tun bayan da Gwamna Uba Sani ya hau mulki a shekarar 2023.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da NIPR bayan taron, musamman wajen inganta ƙwarewa, bin ƙa’idojin aikin hulɗa da jama’a da kuma sadarwa mai inganci.

Source: Original
Gwamnatin Kaduna ta dakatar bikin 'yancin kai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta sanar da dakatar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Kwamishinan yada labarai na Kaduna ya ce gwamnati na nadamar duk wata matsala da matakin zai iya jawo wa jama’a.
Asali: Legit.ng
