Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama da Ake Zargin da Sojoji ne Ya Yi Hatsari a Najeriya

Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama da Ake Zargin da Sojoji ne Ya Yi Hatsari a Najeriya

Ondo, Nigeria - Rahotannin da muka samu yanzu sun nuna cewa wani jirgin helikwafta d ake zargin na sojojin Najeriya ne ya yi hatsari a Igbokoda, hedikwatar Karamar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Litinin a Larada Street da ke Ilaje, inda rahotanni suka ce jirgin ya fada cikin kogi.

Jirgin sojin sama.
Jirgin helikwafta na rundunar sojojin saman Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Air Force
Source: Twitter

Shugaban Karamar Hukumar, Maurice Oripelaye, wanda ya yi magana da manema labarai ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Independen ta rahoto.

Ya ce an gano kayayyakin soji a wurin da jirgin ya fadi, amma ba a iya tabbatar da adadin jami’an da ke cikinsa ba, saboda jirgin ya kone kurmus.

Karin bayani na nan tafe..

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262