Google ya bayyana jihohi 10 na Najeriya da 'yan luwadi suka fi yawa a shekarar 2019
- Duk da dokar dake haramta mu'amalar auratayya ko lalata da jinsi daya a Najeriya, akwai yuwuwar hauhawar wannan lamarin inji Google
- Jihohin Kudu maso yamma ne kan gaba wajen neman fina-finan batsa a Google
- Jihar Imo ce kan gaba inda take biye da Enugu, Anambra, Abia, Delta, Edo, Ribas, Abuja, Legas da kuma Bauchi
Duk da dokar dake haramta mu'amala tsakanin jinsi daya a Najeriya, Google ta bayyana cewa akwai yuwuwar cigaba da mu'amalar jinsi tare da hauhawa a Najeriya.
An kafa dokar ne a 2014 zamanin mulkin Goodluck Jonathan. Dokar ta hana auren jinsi daya, wata dangantakar auratayya da kuma zama dan kungiyar luwadi ko madigo. Akwai hukuncin shekaru 14 a gidan yari da aka tanadarwa masu aikatawa.
Amma kiyasin da Google ta fitar a 2019 ya nuna cewa jihohin kudu maso gabas ne suka fi yawan neman fina-finan batsa na tsakanin jinsi daya a Najeriya. Jihohin Kudu kudu ne ke biye.
Jihar Imo ce kan gaba inda Enugu, Anambra, Abia da Delta ke biye.
Babban birnin tarayya Abuja ne a lamba ta takwas, sai jihar Legas dake biye a ta tara.
KU KARANTA: Tirkashi: Likita ya haramtawa mata mai shekaru 36 haihuwa, bayan ta haifi 'ya'ya 44 a duniya
Ga jihohin dai a jere:
1. Imo
2. Enugu
3. Anambra
4. Abia
5. Delta
6. Edo
7. Ribas
8. Abuja
9. Legas
10. Bauchi
Kamar yadda kiyasin ya nuna, jihohi hudu na yankin Kudu maso gabas ne a kan gaba yayin da jihohi uku na Kudu kudu ke biye. Jihar Arewa daya ce kacal ta samu shiga wannan jerin.
Hakazalika, YouTube ta fitar da kiyasin ta na neman fina-finan batsa amma na jinsi daya.
Jihohin Anambra, Edo, Oyo, Legas da Abuja ne suke kan gaba.
Hakazalika, adireshin yanar gizo na fina-finan batsa ya bayyana cewa matan Najeriya ne suka fi kai ziyara a 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng