Gwamnatin Tinubu Ta Fara Bayani kan Kudin Cire Tallafin Fetur, Ta Fadi Yadda Ta Kashe $500m
- Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu dala miliyan 500 ba tare da karɓar bashi ba domin sake gina filin jirgin sama na Legas
- Festus Keyamo ya danganta ƙarin kuɗaɗen da aka samu da ajiyar kuɗin waje da sauye-sauyen tattalin arziki bayan cire tallafin man fetur
- Ministan ya ce ƙarin masu zuba jari daga kasashen waje zai taimaka wajen samar da kuɗaɗe, ababen more rayuwa da guraben aikin yi ga ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Gwamnatin Tarayya ta ce kudaden da ta samu bayam cire tallafin man fetur sun taimaka mata wajen tara kusan dala miliyan 500 domin sake gina filin jirgin sama na Legas.
Ministan Harkokin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 a Legas.

Source: Facebook
Festus Keyamo ya yi magana ne yayin bikin cika shekaru 67 da kafuwar kamfanin jirgin sama na Aero Contractors, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Keyamo ya ce kuɗin ba a samo su ne ta hanyar karɓar bashi ba, sai dai sun samu ne sakamakon ingantuwar kuɗaɗen da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayar Manajan Daraktan Aero Contractors kan yadda harkar sufurin jiragen sama ke tafiya a ƙarƙashin shirin gwamnatin Tinubu na Renewed Hope Agenda.
Keyamo ya danganta kuɗin da cire tallafin fetur
Keyamo ya ce ikon gwamnati na aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa na da alaƙa da sauye-sauyen tattalin arziki da suka biyo bayan cire tallafin man fetur.
Ya ce gwamnatin ta samu damar tara dala miliyan 500 domin aikin filin jirgin saman Legas ne saboda ingantuwar yanayin kuɗaɗen ƙasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Mu faɗi gaskiya. A bar abin da ’yan siyasa ke faɗa, domin mu duka ’yan siyasa ne. Amma abin da nake cewa shi ne, a zahiri, haka abin ya faru."
“Shugaban ƙasa ya tara dala miliyan 500 domin sake gina filin jirgin saman Legas. Ba kuɗin da aka ci bashi ba ne, saboda mun samu damar yin abin da ya kamata. Kuɗaɗen mu sun ƙaru."
“Asusun ajiyar kuɗin kasashen waje ma ya ƙaru daga dala biliyan 3 zuwa dala biliyan 56 a yanzu. Masu zuba jari kuma suna shigowa Najeriya saboda yanzu sun ga ƙasar tana da damar bunƙasa.” In ji shi.
Ana ci gaba da muhawara kan cire tallafin fetur
Jawaban Keyamo na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da muhawara kan illolin tattalin arziki da suka biyo bayan cire tallafin man fetur.
Masu sukar matakin sun ce manufofin sun ƙara wa ’yan Najeriya wahala, musamman sakamakon hauhawar farashin abinci, sufuri da sauran muhimman kayayyaki.
Sai dai Keyamo ya kare matakin gwamnatin, yana mai cewa ingantuwar muhimman alamomin tattalin arziki da ƙarin ajiyar kuɗin waje na da muhimmanci wajen jawo masu zuba jari da samar da ayyukan yi.

Source: Facebook
Kwankwaso da Obi za su dawo da tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.
Kwankwaso ya ce gwamnatin jam’iyyar ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban.
Asali: Legit.ng

