Mutanen Gari Sun Fadi Abin da Ya Faru lokacin da Jirgin Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari

Mutanen Gari Sun Fadi Abin da Ya Faru lokacin da Jirgin Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari

  • Wani mazaunin Igbokoda ya ce ya ji wata “karar fashewa mai matukar karfi” jim kadan kafin jirgin sojoji ya yi hatsari a yankin
  • Jirgin ya yi hatsarin ne ranar Litinin, 5 ga Oktoba, a wani wuri mai fadama kusa da sansanin sojojin ruwa da ke Igbokoda
  • An ce ‘yan sanda da jami’an soji sun isa wurin domin fara aikin ceto, amma zuwa wurin ya kasance mai wahala saboda yanayin wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Mazauna garin Igbokoda da ke Jihar Ondo sun fara bayyana yadda suka ji lokacin da jirgin helikwafta na rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a kusa da su.

Wani mazaunin garun ya ce ya ji wata “karar fashewa mai matukar karfi” jim kadan kafin jirgin saman ya yi hatsari a yankin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare: NAF ta fitar da cikakken bayani kan jirgin saman da ya yi hatsari a Najeriya

Ondo.
Taswirar jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta rahoto cewa helikwaftan ya yi hatsari ne ranar Litinin, 5 ga Oktoba, a wani wuri mai fadama kusa da sansanin sojojin ruwa da ke Igbokoda, hedkwatar Karamar Hukumar Ilaje ta jihar Ondo.

Yadda mutane suka ji karar fashewa

Magidanci, wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce karar ta fito ne daga yankin da hatsarin ya afku, amma ba su iya zuwa wurin ba saboda yanayin wurin.

“Mun ji wata karar fashewa mai matukar karfi a yankin da lamarin ya faru, amma ba mu iya zuwa wurin ba saboda wurin fadama ne da ke cikin rafin; abin da muke yi kawai shi ne kallonsa daga nesa,” in ji mutumin.

Ya ce daga bisani jami’an ’yan sanda da sojoji sun isa wurin domin fara aikin ceto, yana mai cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin mutanen da ke cikin helikwaftan sun mutu sakamakon hatsarin.

“Amma daga baya ’yan sanda da jami’an soji sun zo wurin domin aikin ceto, sai dai akwai yiwuwar mutanen da ke cikin helikwaftan sun mutu a wurin,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Jirgin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari, ana fargabar mutane da dama sun mutu

NAF ta tabbatarda hatsarin

Vanguard ta rawaito cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta tabbatar da cewa jirgin mallakin sojoji ne, inda ta ce yana kan hanyarsa daga Benin, babban birnin Jihar Edo, zuwa Legas lokacin da hatsarin ya faru.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya kuma bayyana cewa fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai ne suke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya afku.

Jirgin NAF.
Jirgin helikwafta na rundunar sojojin saman Najeriya Hoto: @NigAirForce
Source: Getty Images

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba.

An ce jirgin ya yi hatsarin ne a wani wuri mai fadama a Igbokoda, lamarin da ya sanya isa wurin da hatsarin ya faru cikin wahala.

Tinubu ya yi magana kan hatsarin jirgi

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhini kan hatsarin jirgin Rundunar Sojojin Sama da ake fargabar mutane 32 sun mutu a yankin Igbokoda na Ondo.

Kara karanta wannan

'Su suke kawo kansu': Pantami kan 'yan TikTok da ke barinsa zuwa Jamilu

Shugaban ƙasar ya kuma umarci Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya da ta fara cikakken bincike nan take domin gano musabbabin hatsarin.

Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, da sauran hafsoshi da sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262