An yi biyu babu: Magidanci ya daddatsa uwar matarsa, sa’annan ya halaka kansa
Wani magidanci ya hau dokin zuciya inda ya yi amfani da adda wajen sassara mahafiyar uwargidarsa a gidanta dake titin Arubayi cikin garin Warri na jahar Delta, daga bisani kuma ya kwankwadi gubar da ta kashe shi.
Jaridar The Nation ta ruwaito wannan lamari ya faru ne jim kadan bayan shiga sabuwar shekarar 2020 kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar. Shaidan yace magidancin ya tafi gidan surukarsa ne dauke da adda da nufin cutar da diyarta da yake aure.
KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige mutane 4 har lahira a babban birnin tarayya Abuja
Sai dai a lokacin da matarsa ta hangi yadda ya shigo gidansu dauke da makami, sai ta ranta ana kare, ta tsere domin ceton ranta, amma mahaifiyarta bata iya guduwa ba sakamakon tana da ciwon kafa, nan take ya shiga saranta har sai da ya mata gunduwa gunduwa.
Rahotanni sun bayyana cewa tun da fari, mahaifiyar bata goyon bayan auren da aka kulla tsakanin diyarta da wannan mutumi da ba’a bayyana sunansa ba, amma bayan sun haifi yara 2 sai aka raba auren, amma mijinta bai hakura ba yana son abin sa, don haka ya dauki alwashin daukan mataki a kanta.
Wani direban Keke Napep da ya ga abin da ya faru yace: “Matar ta tsere, amma mahaifiyarta bata iya guduwa sakamakon tana da ciwon kafa, nan take ya shiga saranta har sai da ta mutu. Duk makwabtansu sun tsere, suna tsoron kada ya far musu, amma daga bisani sai ya sha guba, inda ya mutu nan take.”
Rudunar Yansandan jahar Delta ta tabbatar da aukuwar mummunan lamarin, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahart, Adeyinka Adelek ya tabbatar, inda yace: “Da gaske ne, mutumin ya kashe kansa.”
Tuni dai an kwashe gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiyan gawarwaki na babban asibitin garin Warri.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng