Tirkashi: Da ya bankawa mahaifiyarshi ciki shege, a yayin da yake gwajin layar bita zai-zai a kanta

Tirkashi: Da ya bankawa mahaifiyarshi ciki shege, a yayin da yake gwajin layar bita zai-zai a kanta

- Wani saurayi dan shekara 19 ya bankawa mahaifiyar shi cikin shege

- Sauraiyin yayi mata cikin ne bayan ya karbo wata layar bita zai-zai a wajen wani boka

- Saurayin ya ce kawai ya tsinci kanshi yana amfani da mahaifiyar shi bai san cewa lamarin zai kai haka ba

Mutanen garin Asaba, cikin jihar Delta har yanzu ba su gama jimamin yadda wani saurayi dan shekara 19 ya dirkawa mahaifiyar shi cikin shege ba, a yayin da yake gwaji na abubuwan surkullen shi.

A yadda rahoton ya bayyana, yaron wanda aka fi sani da Ekenem, an ce yaje wajen wani boka, wanda ya bashi laya da idan yana amfani da ita mata za su so shi, dama dai can saurayin yana da niyyar yin amfani da layyar akan mahaifiyarshi da kuma wata budurwa da take a makarantarsu.

An bayyana cewa mijin matar wanda yake daukar lokaci ba tare da ya dawo gida ba idan ya tafi wajen harkokinsa a garin Fatakwal ya bayyana cewa cikin ba nashi bane a lokacin da jami'an tsaro ke gabatar da bincike.

Amma kuma mahaifiyar yaron a lokacin da take magana da manema labarai ta ce: "Ban san yadda lamarin ya faru ba, amma dai abinda zan iya cewa shine, wani saurayi mai kama da dana ya shigo dakina, ina ganin shi amma na kasa cewa mishi komai har yayi abinda zai yi ya gama," in ji matar.

KU KARANTA: Kano: Magidanci ya zubawa danshi shinkafar bera ya mutu, saboda ya haifeshi ba ta hanyar aure ba

Haka shi ma saurayin da ake zargin da yake magana da manema labarai ya ce; "Ina mai bayar da hakuri akan lamarin da ya faru, ban taba tunanin lamarin zai kai haka ba, na samu kaina cikin matukar soyayyarta bayan an hada mini maganin matan. Dole na fadi gaskiya, saboda na san Allah zai iya sanya mata hakuri a cikin zuciyarta ta yafe mini. Kawai na tsinci kaina ina kwanciya da mahaifiyata, a yayin da nake tunanin surkullen da aka bani baya aiki, nayi kokarin kashe ta amma sai aka kai lamarin ga 'yan sanda," in ji shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Celestina Kalu, ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace tuntuni aka kama saurayin bayan anji yayi yunkurin kashe mahaifiyar ta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel