Kotun zabe: Sanata Omo Agege ya jinjinawa mutanen Jihar Delta da Najeriya

Kotun zabe: Sanata Omo Agege ya jinjinawa mutanen Jihar Delta da Najeriya

Mun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya yabawa mutanen yankinsa na Delta ta tsakiya da sauran mutanen Najeriya da su ka tsaya masa lokacin da ake shari’arsa.

Sanata Ovie Omo-Agege ya samu nasara a gaban kotun da ke sauraron karar zaben kujerar majalisar dattawa na Mazabar Delta ta tsakiya. Agege ya ce hukuncin sam bai zo masa da mamaki ba.

Omo-Agege ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Mista Yomi Odunuga. A jawabin da Odunuga ya fitar, Sanatan ya yi alkawarin cigaba da yi wa jama’ansa aiki.

A cewar Sanatan na APC, tun farko karar da aka kai game da zaben da ya lashe, bata lokaci ne, domin kuwa ya ce dubban mutane na Mazabar jihar Delta ta tsakiya sun kada masa kuri’a a zaben 2019.

KU KARANTA: Abin da ya sa Tauraro Nabaraska ya fita daga harkar Kannywood

‘Dan majalisar ya yi kira ga jama’an na sa su cigaba da hada kai domin ganin yadda zai kawo ayyukan da za su yi masu tasiri. Omo-Agege ya ke cewa kuliya sun tabbatar da cewa shi ya ci zabe.

Hadimin Sanatan ya ke cewa "Sanata mai-ci ya doke ta a akwatin zabenta, da Mazabarta, har ma da karamar hukumarta. Ya ke cewa: "Dole aka yi watsi da karar domin an gaza gamsar da Alkalan kotu."

“Sanata Ovie Omo-Agege da jam’iyarsa ta APC ba su yi mamaki samun wannan nasara a kotu ba. Sanata ya yi kira ga Mabiya da Ma’aikatansa su ajiye murna su dauki manufofinsa na halin girma” Inji Odunuga.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng