Rikicin APC a Jihar Kano Ya Fara Fitowa, An Aika Sako Mara Dadi ga Shugaba Tinubu
- Gabanin babban zaben 2027, Aminu Shehu Uba Sharada ya nemi Bola Tinubu da Abdulaziz Yari su sasanta shugabannin APC a Kano
- Sharada ya ce akwai rashin jituwa da rarrabuwar kai tsakanin wasu shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC a jihar
- Ya yi gargadin cewa rashin magance matsalolin cikin gida tun kafin zaben 2027 na iya haifar da mummunan sakamako ga jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Yayin da ake kara kusantar babban zaben 2027, wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Aminu Shehu Uba Sharada, ya nemi a yi zama domin sasanta jiga-jigan jam'iyya mai mulki
Ya roki Shugaba Bola Tinubu da Sanata Abdulaziz Yari su hada shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano domin sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027

Source: Twitter
Rikicin APC ya fara fitowa a Kano
Leadership ta ruwaito cewa Sharada, wanda ke aiki a matsayin mai taimaka wa Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa, ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa.
Ya bayyana damuwa kan abin da ya kira rashin jituwa da rabuwar kai da ake gani tsakanin masu ruwa da tsaki na APC a Kano, yana mai gargadin cewa rashin magance matsalolin kafin zaben 2027 na iya haifar da mummunan sakamako.
Sharada ya kuma yi gargadin bai kamata wasu suka fadawa Tinubu cewa APC a dunkule take a Kano alhali kuwa, a cewarsa, akwai wasu batutuwan da ba a warware su ba tsakanin manyan masu ruwa da tsaki.
Jigon APC ya aika sako ga Tinubu
Ya ce:
“Bari in yi magana a fili: duk wanda yake gayawa shugaban kasa cewa komai yana tafiya daidai a cikin APC ta Kano, ba gaskiya yake gaya masa ba.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
“Akwai rashin jituwa da damuwa da ake iya gani tsakanin shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki, kuma idan ba a magance su da wuri ba, za su iya haifar da mummunan sakamako ga jam’iyyar.”
Ya ce kusantowar zaben 2027 ya sa ya zama wajibi shugabannin jam’iyyar na kasa su fara tuntuba da sulhu da masu ruwa da tsaki a Kano.
“Wannan ba lokacin bangaranci ko kara zurfafa rabuwar kai ba ne. Lokaci ne na tuntuba, sulhu da kuma shiga harkokin siyasa na gaskiya,” in ji Sharada.

Source: Facebook
A cewarsa, dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suna da alhakin sake gina amincewa da hada bangarori daban-daban da ke cikin jam’iyyar wuri guda.
Sharada ya ce har yanzu APC tana da dimbin mambobi da masu ruwa da tsaki masu kishin jam’iyyar a Kano, amma tana bukatar shugabanci mai hada kowa da kowa wanda zai saurari damuwar bangarori daban-daban.
Doguwa ya yi maganar hadin kan APC
Kun ji cewa ɗan majalisar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya ce sabon sauyin siyasa da hadin kan APC zai karfafa damar jam’iyyar a Kano a zaben 2027.
Ya bukaci mambobin APC da magoya bayanta su yi aiki tare a matsayin iyali domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.
Asali: Legit.ng