Da dumi-dumi: Yanzun nan yan bindiga sun kai hari wata makaranta, sun yi garkuwa da yan gida daya

Da dumi-dumi: Yanzun nan yan bindiga sun kai hari wata makaranta, sun yi garkuwa da yan gida daya

Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Litinin, 14 ya watan Oktoba, sun kai farmaki a yankin Issele-Azagba kusa da Asaba, jihar Delta sannan suka sace yara biyu daga wata makarantar kudi.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmaki harabar makarantar da misalin karfe 10:00 na safe cikin bakar mota kirar SUV.

Sun yiwa masu tsaron makarantar mugun duka sannan suka daure su, kafin kai tsaye suka tafi ajin da yaran suke wadanda suka kasance uwa daya-uba daya inda suka tafi da su.

A cewar Wata majiya, “yan bindigan na ta harbi a iska yayinda suke rike da yaran, domin tsoratar da mutane."

Majiyar ya nuna al’ajabin yadda masu garkuwan suka yi nasarar yiwa masu tsaron makarantar dukan tsiya.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton an tattaro cewa ana kan kokarin jin ta bakin hukumar makarantar.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda ya kaiwa Oshiomhole hari – Kwamishinan yan sandan Edo

Da aka tuntube shi, kwamishinan yan sandan jihar, Mista Adeyinka Adeleke bai iya tabbatar da lamarin ba.

Yace: “jami’aina na fili a yanzu suna aiki don haka ba zan iya tabbatar da komai ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel