Hukumar NDDC ta raba kwangilolin bogi na fiye da N1tr a shekara 3 – Darekta

Hukumar NDDC ta raba kwangilolin bogi na fiye da N1tr a shekara 3 – Darekta

Kwamitin shugabannin rikon kwaryar da aka nada domin su kula da hukumar NDDC sun fara bankado wasu badakaloli da aka yi.

A Ranar 15 ga Watan Junairun 2020, kwamitin nan ya bayyana yadda aka bada kwangilolin Naira tiriliyan daya ba tare da bin doka ba.

Mukaddashin Darektan ayyuka wanda shi ne shugaban kwamitin binciken kwangiloli na NDDC, Cairo Ojougboh, ya fadi wannan.

Dr. Cairo Ojougboh ya bayyanawa Manema labarai jiya cewa babu takardu ko zanen ayyukan duk kwangilolin da aka rika badawa.

Haka zalika, Cairo Ojougboh, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa babu kudin wadannan kwangiloli da aka raba a cikin kasafin kudin hukumar.

KU KARANTA: Ana tsoron binciken da Shugaba Buhari zai yi a NDDC - Minista

A cewar Mukaddashin Darektan kwangilolin, binciken da su gudanar ya nuna an yi wannan barna ne daga shekarar 2016 zuwa 2019.

“Alal misali a 2017, hukumar ta bada kwangilolin kar-ta-kwana 201 a kan N100.4b. A 2018, an bada kwangiloli 1, 057 a kan kudi N162.69b.”

“A cikin watanni bakwai na 2019 kacal, an raba kwangiloli 1,921 wanda su ka ci N1.07t. Ana maganar N1.3t ne a kasa da shekaru uku”

“Kasafin NDDC a shekara ba ya wuce N400b. Inda za a bada aikin bogi na Tiriliyan a shekara guda, ya nuna cewa an sace kudin komai ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel