'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Harbi Tawagar 'Yan Kasuwa a Filato

'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Harbi Tawagar 'Yan Kasuwa a Filato

  • ’Yan bindiga sun bude wa wata motar da ke dauke da ’yan kasuwa wuta a jihar Plateau, lamarin da ya jikkata mutane bakwai a yankin Jos ta Kudu
  • ’Yan kasuwar na kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwa ne lokacin da maharan suka bude musu wuta a kusa da hanyar Bukuru
  • Rundunar ’yan sandan jihar Plateau ta ce an tura jami’an tsaro domin karfafa tsaro a yankin tare da fara farautar wadanda suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau – Rundunar ’yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da cewa mutane bakwai sun jikkata bayan da wasu ’yan bindiga suka bude wa wata motar ’yan kasuwa wuta a hanyar Bukuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026, yayin da ’yan kasuwar ke dawowa daga Kasuwar Kara da ke Bukuru.

Kara karanta wannan

Sama da mutane 30 sun mutu da hatsarin jirgi ya rutsa da masu zuwa jana'iza a Najeriya

Taswirar jihar Filato
Taswirar jihar Filato a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

’Yan bindiga sun bude wuta

Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Alfred Alabo, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa motar da aka kai wa harin na dauke da ’yan kasuwa ne da ke dawowa daga Kasuwar Kara.

Ya ce an gano mutane bakwai da suka samu raunuka, wadanda aka kai su Asibitin Sojoji da ke Rukuba a Jos domin samun kulawar likitoci.

Rundunar ta yi Allah-wadai da harin, inda ta bayyana shi a matsayin mummunan lamari tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

'Yan sanda sun fara binciken harin

Kwamishinan ’yan sandan jihar Plateau, CP Ayodeji Faniyan, ya umarci mataimakin kwamishinan ’yan sanda mai kula da sashen bincike da ya jagoranci binciken lamarin.

Rundunar ta ce za a yi kokarin gano wadanda suka kai harin tare da cafke su domin fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

An yi wa tsohuwar shugabar matan APC kisan gilla a gidanta da ke Bauchi

Haka kuma, an tura rundunonin musamman da na yaki da fashi da makami domin kara tsaurara tsaro a yankin, yayin da jami’an leken asiri ke kara tattara bayanai kan wadanda ake zargi.

Jami'an ’yan sanda sun yi gargadi

Rundunar ta shawarci mazauna jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na halal, amma su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro.

Ta bayar da lambobin gaggawa na dakin kula da ayyukan ’yan sanda, wato 07059473022 da 08038907662, domin jama’a su kai rahoton abubuwan da suka shafi tsaro.

Tunji Disu a wajen taro
Sufeton 'yan sanda, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa rundunar ta kuma bayar da wasu lambobi domin kai rahoton rashin da’a daga jami’anta, ciki har da ACP X-SQUAD – 08034448617, PPRO – 08060545670, CRU – 08037681026 da PCB – 09016146804.

An kashe shugaban ISWAP

A wani lamarin, kun ji cewa wani babban shugaban kungiyar ISWAP, Abdussamad Ohida, wanda aka fi sani da Anwar, ya mutu a wani samame da hadin gwiwar sojojin Najeriya, DSS da Amotekun suka kai a dajin Owo na jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Majiyoyin tsaro sun ce Ohida yana dab da shirya manyan hare-haren ta’addanci a wasu jihohin kudancin Najeriya, musamman hare-haren da ake zargin za a kai kan fararen hula.

An ce Ohida ya taba zama mataimakin Abu Ikrimah, wanda aka fi sani da Abu Uwais, shugaban ISWAP a wasu yankunan Najeriya, kafin DSS ta kama Abu Uwais a shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng