Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe Shugaban PDP a Delta

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe Shugaban PDP a Delta

Wasu da ake zargin masu kisan gilla ne sun harbe Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Ward 4 (Olomu Ward 1) da ke yankin Ughelli ta Kudu a jihar Delta, Mista Paul Onomuakpokpo.

Rahotanni sun kawo cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Laraba, 8 ga watan Janairu a hanyar Ogoni, kusa da fadar Ohworode na masarautar Olomu.

A nan take marigayin ya mutu bayan makasan nasa sun harba masa alburusai da dama.

Motarsa kirar Toyota Camry duk ta kasance dauke da harbin bindiga.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan na ta harbi ba kakkautawa a sama sannan sai da suka tabbatar marigayin ya mutu kafin su bar wajen.

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan jihar Delta ta tabbatar da lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Hafiz Inuwa ya ce, “gaskiya ne. An kai gawar wajen ajiye gawawwaki. Kuma muna bincike cikin lamarin.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na Kogi ta yamma, Mista Taiwo Kola-Ojo ya mutu.

Ojo ya yanke jiki ya fadi sannan ya mutu a yammacin ranar Talata, 7 ga watan Janairu yayinda ya ke buga wasan Kwallo na tennis.

Babban sakataren PDP na jihar Kogi, Bode Ogunmola wanda ya tabbatar da mutuwar a wani jawabi a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu ya bayyana mutuwar Kola-Ojo a matsayin abun bakin ciki kuma wanda ya zo a bazata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng