Tashin Hankali: Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Mutane 70 a Hanyar Dawowa daga Jana'iza
- Jirgin ruwa na katako dauke da masu ta'aziyya sama da 70 da babura fiye da 30 ya kife a kogin Katsina-Ala da ke Buruku a Jihar Benue
- An ceto mutane da dama bayan jirgin ya kife, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman wadanda ba a gano inda suke ba
- Shugaban Karamar Hukumar Buruku ya ce akalla mutane shida ba a gan su ba, yayin da aka ceto sama da 60
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Jirgin ruwa na katako dauke da masu makoki sama da 70 da babura fiye da 30 ya kife a safiyar Asabar yayin da yake tsallaka kogin Katsina-Ala a mashigar Buruku ta Karamar Hukumar Buruku a Jihar Benue.
Lamarin ya faru da misalin karfe 11 na safe, lokacin da fasinjojin, wadanda akasari suka fito daga Mbayon a Karamar Hukumar Gboko, suke dawowa daga jana’izar wani dan uwansu da aka yi a dayan gefen kogin.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: 'Yan ta'adda sun rutsa manoma 15, sun masu mummunan aiki babu daɗin gani

Source: Getty Images
Vangaurd ta ce an ce an ceto fasinjoji da dama bayan faruwar lamarin, yayin da aka ci gaba da aikin bincike da ceto da yammacin Asabar domin gano wadanda suka bata.
Abin da ya jawo hatsarin jirgin
Wani ganau a yankin ya ce jirgin ruwan ya yi matukar cika da kaya fiye da karfinsa lokacin da injinsa ya samu matsala a tsakiyar tafiyar.
A cewarsa:
“An yi cika jirgin da mutane da dama da kuma babura fiye da 30, kuma suna dawowa ne daga bangaren Karamar Hukumar Logo na kogin da misalin karfe 11 na safe lokacin da lamarin ya faru.
“An ceto mutane da dama, amma a halin da ake ciki ba zan iya gaya muku ainihin adadin mutanen da ba a gani ko cetowa daga kogin ba saboda har yanzu ana ci gaba da bincike. Amma mutane da dama ba a gan su ba a yanzu.”
An ceto mutane 60 daga ruwa
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Buruku, Mista Raymond Zege, ya ce wadanda abin ya rutsa da su suna cikin alhini bayan sun dawo daga jana’iza.
Shugaban karamar hukumar ya ce har yanzu ba a tantance ainihin adadin fasinjojin da suka bace ba, yana mai cewa ma’aikatan ceto sun riga sun ceto mutane da dama.
“Yanzu ba mu san adadin mutanen da suka bace ba. Ya zuwa yanzu ba mu ga kusan mutane shida ba, amma mun ceto sama da 60. Aikin bincike da ceto yana ci gaba,” in ji shi.
Gwamnatin Benue kwantar da hankali
Kwamishinan Ruwa da Tattalin Arzikin Shudi na Jihar Benue, Hon. Denis Iyaghigba, ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa ranar Asabar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Source: Original
AYa ce:
“Na samu rahotannin farko kan wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a mashigar Buruku a safiyar yau, Asabar, 3 ga Oktoba, 2026.
“Ina tabbatar wa jama’a, musamman iyalan wadanda ke cikin jirgin, da su kwantar da hankalinsu su kuma jira sahihan bayanai daga hukumomin da suka dace. Ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu.”
Jirgin ruwa ya kife a Jigawa
Kun ji cewa matafiya mata huɗu sun mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutane takwas ya kife a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Bayanai sun nuna cewa iska mai ƙarfi da ake yi a lokacin da lamarin ya auku na cikin abubuwan da suka haddasa hatsarin.
Asali: Legit.ng

