Tirka tirkan zabe: Alkalan kotun Koli sun halasta zaben gwamnonin Neja, Abia da Delta

Tirka tirkan zabe: Alkalan kotun Koli sun halasta zaben gwamnonin Neja, Abia da Delta

Karshen tika tika tik! Biyo bayan doguwar tirka tirka a gaban kotuna daban daban, daga karshe kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da gwamnonin jahohin Neja, Delta da Abia suka samu a yayin zaben gwamnoni na shekarar 2019.

Jaridar Punch ta ruwaito Alkalan kotun sun fara ne da shari’ar gwamnan Neja, Abubakar Bello Abu Lolo, inda kotun ta yi fatali da korafin da dan takarar gwamnan jahar a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Mohammed Nasko ya shigar gabanta.

KU KARANTA: Murna ta koma ciki: Za mu sake bude binciken tsohon gwamnan jahar Ribas – EFCC

Tirka tirkan zabe: Alkalan kotun Koli sun halasta zaben gwamnonin Neja, Abia da Delta
Gwamnonin Neja, Abia da Delta
Asali: Facebook

Nasko ya shigar da korafin ne yana kalubalantar nasarar da Gwamna Abu Lolo na jam’iyyar APC ya samu a zaben watan Maris na shekarar 2019, inda ya yi zargin an yi aringizon kuri’u a alkalumman da suka baiwa Abubakar nasara.

Haka zalika Alkalan sun tabbatar da halascin zaben gwamnan jahar Delta, Ifeanyi Okowa, sa’annan suka yi fatali da karar da dan takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyyar APC, Great Ogboru ya shigar gabanta, inda ya kalubalanci nasarar Okowa.

Bugu da kari, duk a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, kotun koli ta tabbatar da igancin zaben daya samar da Mista Okezie Ikpeazu a matsayin zababben gwamnan jahar Abia, tare da halasta nasarar daya samu a zaben.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kotun ta yi fatali da karar da dan takarar gwamnan jahar a karkashin inuwar jam’iyyar APGA, Alex Otti ya daukaka zuwa gabanta, inda ta ce karar tasa bata da tushe balle makama sakamakon ya gaza wajen gabatar da kwararan hujjoji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel