Ashsha! Yan fashin teku sun yi garkuwa da mutane 3, sun kashe Sojojin Najeriya 3

Ashsha! Yan fashin teku sun yi garkuwa da mutane 3, sun kashe Sojojin Najeriya 3

Gungun yan bindiga dake fashi a kan teku sun halaka zaratan dakarun rundunar Sojin ruwan Najeriya guda hudu daga cikin Sojoji shida da suka kai agajin gaggawa ga wani babban jirgin ruwa da yan bindigan suka tare.

Premium Times ta ruwaito yan bindigan sun kashe Sojojin ne a yayin musayar wuta da aka yi a ranar 2 ga watan Janairu da misalin karfe 11 na dare a tsakiyar ruwan Warri dake jahar Delta.

KU KARANTA: Komai ta fanjama: An umarci Yansandan Najeriya su zama cikin shiri bayan kisan Janar Soleimani

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da fari yan fashin sun tare jirgin dankaro mallakin kamfanin MV AMBIKA dake aikin dakon man fetir a daidai mashigar tafkin Ramos, hakan ne yasa aka tura Sojojin guda 6 domin fatattakar yan bindigan.

Sai dai ko kafin Sojojin su isa, yan bindigan sun shige cikin jirgin, har sun kama mutane uku da suka hada da yan kasar Rasha guda uku, da kuma dan kasar Italiya guda 1. Isarsu ke da wuya sai yan bindigan suka bude musu wuta daga sama.

Bayan sun kashe Sojojin, yan bindigan sun tsere da jirgin tare da mutane ukun da suka yi garkuwa dasu, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

A wani labarin kuma, a wani mataki na kan da garki, ko kuma kamar yadda masu iya magana kan ce, wai “rigakafi ya fi magani” Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an Yansandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam!

IG Adamu ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan kisan wani babban kwamandan yaki na kasar Iran da gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a makon da ta gabata, inda yace sun samu labarin akwai wasu dake shirin tayar da hankulan jama’a a Najeriya tare da yi ma gwamnatin Najeriya zagon kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel