Tinubu Ya Yi Maganar Hatsarin Jirgin Saman Sojoji a Ondo, Ya Bayar da Umarni
- Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhini kan hatsarin jirgin Rundunar Sojojin Sama da ya yi sanadin mutuwar mutane 32 a yankin Igbokoda na Ondo
- Tinubu ya umarci Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta fara cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin tare da hana sake faruwar irin sa
- Shugaban ƙasar ya yaba da aikin ceto da aka fara nan take, tare da jajanta wa iyalan fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna matuƙar alhini kan hatsarin wani jirgin Rundunar Sojin Sama da ya afku kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa a yankin Igbokoda na Jihar Ondo.
Shugaban ƙasar ya kuma umarci Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya da ta fara cikakken bincike nan take domin gano musabbabin hatsarin.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare: NAF ta fitar da cikakken bayani kan jirgin saman da ya yi hatsari a Najeriya

Source: Twitter
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Jirgin yana kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas
A cewar sanarwar, jirgin na Rundunar Sojojin Sama, mai ƙirar ATR-42, yana gudanar da wani aiki na yau da kullum daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya afku.
Mutane 32 ne ke cikin jirgin, waɗanda suka haɗa da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai.
Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, da sauran hafsoshi da sojoji maza da mata na Rundunar Sojojin Sama.
Tinubu ya ce lokaci ne mai raɗaɗi ga Najeriya
A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya ce hatsarin ya kasance babban abin raɗaɗi ga Rundunar Sojojin Najeriya da kuma ƙasar baki ɗaya, The Punch ta kawo labarin.
“Wannan lokaci ne mai raɗaɗi ga Rundunar Sojojin Najeriya da kuma ƙasar baki ɗaya. Jami’an Rundunar Sojojin Sama suna sadaukar da rayukansu a kullum domin kare Najeriya. Ba za mu taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.”
Tinubu ya ce Babban Hafsan Sojin Sama ya yi masa bayani kan hatsarin, sannan ya umarci rundunar ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin da kuma hana sake faruwar irin wannan lamarin nan gaba.
An fara aikin ceto nan take
Shugaban ƙasar ya yaba wa Rundunar Sojojin Sama saboda kunna aikin bincike da ceto nan take bayan faruwar hatsarin.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ji ƙan jami’an da suka rasa rayukansu, tare da ba iyalansu da Rundunar Sojin Sama ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.
Tinubu ya tabbatar da goyon bayan gwamnati
Shugaban ƙasar ya tabbatar wa Rundunar Sojojin Sama da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba ta goyon baya yayin da take gudanar da muhimmiyar rawar da ta taka wajen kare ƙasar.
Tinubu ya kuma yaba da gaggawar martanin jami’an agaji da sauran waɗanda suka fara aikin ceto, da kuma Gwamnatin Jihar Ondo bisa matakan da suka ɗauka a wurin da hatsarin ya faru.

Source: Original
Mutane 32 na cikin jirgin sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, SAN, ya tabbatar da hatsarin wani jirgin soji a Igbokoda, jihar Ondo, wanda ke ɗauke da mutane 32.
Keyamo ya ce jirgin mai lambar rajista NGR 931 ya bace ne yayin da yake kan hanyar Benin zuwa Lagos da misalin ƙarfe 9:13 na safe.
Asali: Legit.ng

