Wata gawurtacciyar yar fashi ta shiga komar jami’an Yansandan Najeriya

Wata gawurtacciyar yar fashi ta shiga komar jami’an Yansandan Najeriya

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Delta sun samu nasarar kama wata gawurtacciyar yar bindiga dake mummunan sana’ar fashi da makami a jahar Delta mai suna Bella Lucky tare da abokan ta’asanta guda biyu.

Jaridar Punch ta ruwaito jarumin dansanda, CSP Anieteh Eyoh ne ya jagoranci samamen kama Bella a abokanta a kasuwar McLivers dake garin Warri, a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Budurwar Sulaiman ta yi masa raddi game da sabuwar bazawarsa baturiya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun dade suna farautar Bella da yaranta biyu sakamakon yadda suka addabi al’ummar garin Warri da kewaye na jahar Delta da sata, kwace da kuma fashi da makami.

Yansanda sun ce sun kwato wayoyin salula da adduna daga hannun Bella a lokacin da suka bi ta har cikin mabuyarta bayan ta caka ma wata mata wuka. Ita dai Bella ta yi kaurin suna wajen janyo hankalin maza zuwa ga yan fashin ta hanyar amfani da Keke Napep.

Da yake tabbatar da kama Bella, kwamishinan Yansandan jahar, CP Mohammed Hafiz Inuwa ya bayyana ma yan jaridu cewa; “Mun kamasu duka uku, guda daga cikin budurwa ce. Wadannan yan fashi ne masu amfani da mace, suna amfani da wuka ne wajen saran mutane suna musu fashi.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da hari a gidan wani babban limamin coci Rabaran Denis Bagauri, wanda ake yi ma inkiya da Fasto Nyako, inda suka bindige shi har lahira.

A daren Lahadi, 19 ga watan Janairu ne yan bindigan suka bi Fasto Denis har zuwa gidansa dake kauyen Nasarawo Jereng, a cikin karamar hukumar Mayo Belwa na jahar Adamawa ne, a can suka karar da rayuwarsa.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce Fasto Denis ya taba zama hadimi ga tsohon gwamnan jahar Adamawa, Murtala Nyako, haka zalika ya taba zama mashawarci ga tsohon gwamnan jahar, Bindow Jibrilla a kan harkokin addini.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng