Wani saurayi da ya shiga kungiyar asiri ya haukace bayan sun nemi ya kai musu mahaifiyarsa ya kasa

Wani saurayi da ya shiga kungiyar asiri ya haukace bayan sun nemi ya kai musu mahaifiyarsa ya kasa

- Wani matashin saurayi ya haukace tuburan, bayan da ya shiga kungiyar asiri suka kuma bukaci ya kai musu mahaifiyarsa

- Matashin ya haukace ne bayan ya kasa kai mahaifiyar tasa, inda aka hango shi yana yawo akan titi kai a birkice

- Lamarin dai ya faru ne a Sapele dake jihar Delta, inda aka bayyana matashin da suna Junior

Wani bidiyo da ya fara yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo ya nuna yadda wani dan damfara na yanar gizo wanda aka fi sani da 'Yahoo Boy', mai suna Junior ya haukace bayan ya kasa kai mahaifiyarsa ayi asiri da ita a jihar Delta.

A yadda rahoton ya bayyana, lamarin marar dadin ji ya faru a Sapele dake jihar Delta, inda aka hango maatashin cikin hauka akan wani titi da mutane ke faman wucewa.

KU KARANTA: Tirkashi: Ta kone gidan saurayinta kurmus saboda yaki yadda ya dinga kwanciya da ita kamar yadda suka yi alkawari

An jiyo shi a cikin bidiyon yana wasu irin maganganu, inda yake cewa, sun bukaci ya kai musu wasu sassan jiki na mahaifiyar tasa, amma ya kasa. Haka kuma ya bukaci sanin dalilin da yasa basu nemi ya kai musu mahaifinsa suyi tsafin da shi ba.

Matasa a Najeriya na kokarin ganin sun yi kudi ta kowacce hanya, yayin da wasu ke shiga kungiyar asiri, damfara, sace-sace, garkuwa da mutane da fashi da makami da dai sauransu, hakan kuma na faruwa ne duk da irin kokarin da jami'an hukumar 'yan sandan kasar ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel