Man fetur: Za mu ba Matatar Dangote gudunmuwa –Timipre Sylva
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin bada gudumuwa ga kamfanin tace man da Aliko Dangote ya ke ginawa. Gwamnatin kasar ta ce za ta rika ba kamfanin duk abin da ake bukata.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnati za ta tabbata Dangote ya samu danyen mai da sauran kayan aiki domin matatarsa ta yi aikin da ake so. Karamin Ministan mai, Timipre Sylva, ya fadi wannan.
Cif Timipre Sylva ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai ziyarar kewaye kamfanin da ake ginawa a Legas. Sylva ya kai wannan ziyara ne tare da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.
Daga cikin ‘yan rakiyar Ministan akwai shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari Kolo da kuma wasu kusoshin kamfanin. Shugaban na NNPC ya yabawa aikin da Aliko Dangote ya ke yi.
A wani jawabi da NNPC ta fitar, Mele Kyari ya ce matatar Dangote za ta taimakawa Najeriya wajen daina shigo da tacaccen fetur. Kamfanin zai sa kudi su ka rika shigowa Najeriya daga ketare.
KU KARANTA: An soma nisa a aikin gyaran kamfanin NNPC na Fatakwal
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na kokarin ganin ranar da Najeriya za ta daina batar da kudi wajen shigo da mai duk da cewa Ubangiji ya yi wa Najeriya tarin baiwar danyen mai.
Idan an kammala wannan kamfani, za a rika tace ganga 650, 000 na danyen mai kullum. Sannan kuma za a samu wasu sinadarai na yin taki da sauransu da za su taimakawa tattalin arziki.
An rahoto ziyarar kewayen Ministan ne a Ranar Litinin 4 ga Watan Nuwamban 2019 ta bakin Mukaddashin mai magana da yawun kamfanin man kasar nan NNPC, Mista Samson Makoji.
Ministan ya na cewa: “Matatar man Dangote katafaren aiki ne da ‘Dan Najeriya ya yi wa ‘Yan Najeriya.” Ana sa ran kammala aikin wannan matata da ke Unguwar Lekki ne a karshen 2020.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng