Da duminsa: Buhari ya sallami mukaddashin shugaban hukumar NDDC

Da duminsa: Buhari ya sallami mukaddashin shugaban hukumar NDDC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada Farfesa Kemebradikumo Daniel a matsayin sabon mukaddashin shugaban hukumar kula da yankin Neja Delta (NDDC).

A cikin wani jawabi da kakakin shugaban Buhari, Femi Adesina, ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa Farfesa Pondei zai maye gurbin mukaddashin shugaban hukumar, Barista Joi Nunieh.

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya amince da fadada shugabancin mutanen da ke kula da hukumar (IMC) daga mutane uku zuwa biyar.

Mutanen biyar da shugaba Buhari ya amince da nadinsu sune kamar haka; Farfesa Kemebradikuma Pondei, Dakta Cairo Ojougboh, Mista Ibanga Bassey Etang, Uwargida Caroline Nagbo da Cecilia Bukola Akintomide.

Sabon mukaddashin shugaban Farfesa ne a likitanci da ke aiki a jami'ar yankin Neja Delta. Kazalika, ya taba rike shugaban tsangayar kimiyyyar lafiya dna jami'ar.

A cikin watan Oktoba na shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin gudanar da binciken kwakwafi ta hanyar amfani da kimiyyar zamani a kan yadda ake sarrafa kudaden da ake bawa hukumar NNDC tun daga shekarar 2001 zuwa 2019.

Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan yawan suka da korafin da ake yi a kan tafka almundahana wajen sarrafa kudaden da gwamnati ke bawa NNDC domin gudanar da aiyukan da zasu ciyar da yankin Neja Delta, mai arzikin man fetur, gaba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel