Jihar Borno
Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawarin biyan kudin fansan duk barnar da Boko Haram ta yi a garin Auno tare da sabunta dukkanin gidajen da suka lalata a garin.
Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar jaje ga mutanen da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai ma hari a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu.
Babban hadimin shugaban kasa a kan harkokin watsa labaru, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa wasu yan siyasa ne suka dauki nauyin biyan yaransu yan bangan siyasa domin su yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a jahar Borno.
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yaba ma gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum, kan kira ga sauya salon tsaron kasar baki dayanta.
Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ihun da wasu mutane suka yiwa shugaban kasa Muhammnadu Buhari a lokacin da ya kai ziyarar jaje a garin Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.
Dan majalisa dake wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza a majalisar wakilan Najeriya, Ahmadu Usman Jaha ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa idan har hakan zai kawo zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno ya bayyana cewa akwai bukatar a sauya salon yakin da ake da yan ta’addan Boko Haram a kasar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha. Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Abba sannan a yanzun nan ya sauka a Maidururi, babbar birnin jahar Borno.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya jadadda bukatar a gudanar da bincike kan harin da yan ta’adda suka kai Auno wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 30.
Jihar Borno
Samu kari