An kama matashi da ya saci litattafan addini fiye da 100 daga masallatai a Maiduguri

An kama matashi da ya saci litattafan addini fiye da 100 daga masallatai a Maiduguri

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno ta tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 21 bisa zarginsa da satar litattafai fiye da 100 a masallatai da ke Maiduguri.

Matashin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne yayin da yako kokarin sake tafka wata satar a wani masallacin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Mohammed Aliyu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa jama'a ne suka kama matashin ranar 7 ga watan Fabrairu.

A cewar kwamishinan, binciken rundunar 'yan sanda ya nuna cewa an taba samun matashin da laifin sace wasu litattafan addini 100 kafin a kama shi.

An kama matashi da ya saci litattafan addini fiye da 100 daga masallatai a Maiduguri
'Yan sandan Najeriya
Asali: Depositphotos

"Ba shi kadai bane, akwai ragowar abokansa da suke fake wa da ibada domin su samu damar sace takalma, agoguna, kudi da wayoyin masu bauta.

"Matashin da bakinsa ya fada mana cewa yana sayar da litattafan, da kowanne darajars ta kai N3,000, a kan N500," a cewar kwamishina Aliyu.

DUBA WANNAN: Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina

Kwamishinan ya jaddada aniyar rundunar 'yan sanda ta kama sauran abokan matashin tare da cigaba da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kazalika, ya yi kira ga masu zuwa wuraren bauta domin yin ibada a kan suke kula da dukiyoyinsu tare da hanzarta sanar da hukuma motsin duk wani mutum ko mutanen da basu yarda da su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel