NiMet: Da Yiwuwar a Zabga Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 3 a Kano da Wasu Jihohi
- Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi daban-daban, ciki har da rana, hadari da ruwan sama a fadin kasar daga Litinin zuwa Laraba
- A wasu jihohin Arewa, ana sa ran za a samu tsawa da matsakaicin ruwan sama tare da kasancewar gajimare na tsawon yini uku
- Hukumar NiMet ta gargadi mazauna yankunan da abin ya shafa da masu ababen hawa kan ambaliyar ruwa, iska mai karfi da zamewar tituna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi daban-daban na tsawon kwanaki uku, ciki har da hasken rana, gajimare, tsawa da ruwan sama a sassan kasar daga Litinin zuwa Laraba.
A cikin hasashen yanayi na kwanaki ukun da ta fitar a Abuja ranar Lahadi, NiMet ta ce ana sa ran samun yanayi mai zafi da hasken rana tare da gajimare lokaci zuwa lokaci a wasu sassan kasar.

Source: Getty Images
Za a yi ruwa da tsawa a Arewa
Hukumar ta ce wasu jihohin Arewa za su iya fuskantar tsawa da matsakaicin ruwan sama a yayin da gajimare zai mamaye sararin samaniya, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Jihohin da hasashen ya shafa sun hada da Taraba, Kaduna, Adamawa, Kano da Borno. Mazauna wadannan jihohi na iya fuskantar sauyin yanayi a lokuta daban-daban cikin kwanaki ukun.
A yankin Arewa ta Tsakiya, ciki har da Babban Birnin Tarayya (FCT), Neja, Plateau, Nasarawa da Benue, NiMet ta yi hasashen samun tsawa da safe da kuma da rana.
Hukumar ta kara da cewa ana sa ran samun matsakaicin ruwan sama a sassan yankin a tsawon lokacin hasashen. Wannan na iya shafar zirga-zirgar ababen hawa da sauran ayyukan yau da kullum, musamman a wuraren da ake samun taruwar ruwa.
Yaya yanayin zai kasance a Kudu?
A jihohin kudancin Najeriya, ciki har da Legas, Ondo, Ogun, Rivers, Bayelsa, Akwa Ibom da Cross River, NiMet ta yi hasashen samun matsakaicin ruwan sama a sassa da dama.
A cewar hukumar, ana iya samun ruwan sama tun da safe a wasu wurare, wanda zai ci gaba zuwa rana da yamma.
Mazauna yankunan kudancin kasar na bukatar kula da sauyin yanayi yayin gudanar da harkokinsu, musamman a wuraren da aka saba samun ambaliya bayan ruwan sama mai yawa.
NiMet ta gargadi masu ababen hawa
Hukumar ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da masu ababen hawa da su dauki matakan kariya daga yiwuwar ambaliyar ruwa kwatsam, iska mai karfi da zamewar kasa a lokacin ruwan sama.
A ruwayar Vanguard, NiMet ta bukaci jama’a su kasance cikin shiri tare da kula da sanarwar yanayi da hukumomin da abin ya shafa ke fitarwa domin rage illolin sauyin yanayi.

Source: Twitter
Masu ababen hawa kuma an shawarce su da su yi taka-tsantsan yayin tuki a lokacin ruwan sama, musamman a wuraren da ake samun taruwar ruwa ko rashin gani sosai.
Hukumar ta jaddada muhimmancin bin ka’idojin tsaro a yayin sauyin yanayi, domin ruwan sama mai karfi na iya haifar da ambaliya da kuma matsalolin zirga-zirga a wasu wurare.
Jihohin da ke fuskantar hadarin ambaliya
A wanai labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi cewa garuruwa 915 da ke jihohi 19 da Abuja na cikin babban hadarin ambaliyar ruwa tsakanin 27 ga Agusta zuwa 9 ga Satumba, 2026.
Gwamnatin ta danganta hasashen hadarin ambaliyar da yawan danshin kasa, ruwan sama mai yawa, saurin kwararar ruwa a saman kasa, cunkoson ruwa a magudanan ruwa da kuma karuwar cikar koguna.
Asali: Legit.ng


