A shirye nake na sadaukar da rai na domin kawo zaman lafiya a Arewa maso gabas – Dan majalisa

A shirye nake na sadaukar da rai na domin kawo zaman lafiya a Arewa maso gabas – Dan majalisa

Dan majalisa dake wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza a majalisar wakilan Najeriya, Ahmadu Usman Jaha ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa idan har hakan zai kawo zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.

Jaha ya bayyana haka ne a zauren majalisar yayin zaman ta na ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu na shekarar 2020, inda yake kokawa bisa harin da yan ta’addan Boko Haram suka kai a karshen makon data gabata a garin Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta binciko fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a Arewa maso gabas

A shirye nake na sadaukar da rai na domin kawo zaman lafiya a Arewa maso gabas – Dan majalisa
Ahmadu Jaha
Asali: Facebook

“Ina fadin wannan ba tare da wani tsoro ba, cewa a shirye nake na mika rayuwata idan har al’ummar dake yankin Arewa maso gabas za su samu zaman lafiya, ni na shirya sadaukar da rayuwana.

“Abu mafi zafi a duniyar nan shi ne kana zaune cikin kwanciyar hankali yayin da al’ummar da kake wakilta suke cikin tashin hankali, ana karkashesu kamar wasu dabbobi.” Inji shi.

Jaha ya danganta harin Auno ga sakacin dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya, saboda a cewarsa Sojoji sun samu labarin akwai yiwuwar samun wannan hari, amma suka yi biris ba tare da daukan wani kwakkwaran mataki ba.

A wani labarin kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.

A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan yan Najeriya, duba da sake farfadowar da Boko Haram ta yi.

Da wannan ne babban hafsan Sojan, Laftanar Janar Tukuru Tusuf Buratai yace: “Ba tare da kalubalantar ikon majalisa ba, amma sallamar hafsoshin tsaro ba shi bane hanyar da zai warware matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da ita.”

Buratai ya kara da cewa Buhari na sane da halin da ake ciki, kuma shi ne mai dakin, shi ya san inda ke masa yoyo, haka zalika shi kadai ne zai iya yanke hukuncin da ya kamata game da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: