Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawarin biyan kudin fansan duk barnar da Boko Haram ta yi a garin Auno tare da sabunta dukkanin gidajen da suka lalata a garin.

Boko Haram sun kai harin ne a makon data gabata bayan Sojoji sun rufe hanyar shiga garin Maiduguri daga karfe 5 na yamma kamar yadda dokar ta baci ta tanada, hakan yasa suka datse jama’a da dama a waje, wadannan jama’an ne Boko Haram ta kai ma farmaki ta karkashesu, sa’annan ta kona motocinsu.

KU KARANTA: Ta leko ta koma: Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito ministar kula da yan gudun hijir da wadanda bala’o’i ya shafa, Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka yayin wani ziyara da ta kai garin Auno dake cikin karamar hukumar Konduga a ranar Alhamis.

Sadiya ta samu rakiyar shugaban hukumar cigaban Arewa maso gabas, Paul Tarfa tare da babban daraktan hukumar, Mohammed Alkali da kuma shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Borno, Gajiya Kolo, inda ta bayyana damuwar shugaba Buhari game da barnar da aka samu a garin.

“Mun zo nan ne a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya umarci ma’aikatata ta kai ziyarar jaje ga jama’an garin Auno sakamakon harin da Boko Haram suka kai muku, shugaban kasa ya umarce ni na tabbatar muku da burinsa na taimakonku.” Inji ta.

Sa’annan ta kara da cewa sun isa garin ne domin gane ma idanunsu matsayin barnar daya auku, tare da tabbatar ma jama’an cewa gwamnati za ta mayar ma kowa duk abin da suka yi asara, hatta gyaran gidajensu da aka kona.

A jawabinsa, daraktan hukumar cigaban yankin Arewa maso gabas, Alkali yace: “A yanzu mun ga halin da ku ke ciki, mun fahimci barnar da aka muku, zamu koma mu shirya tsaf domin dawowa mu baku kulawar da ta kamata tare da sake gina rayuwarku.”

Shi ma hakimin garin Auno, Abba Umar ya jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari game da ziyarar daya kai jahar Borno domin jajanta ma al’ummar jahar sakamakon abin da ya faru, sa’annan ya bayyana damuwarsa game da jama’an da suka rasa muhallansu da hanyoyin cin abincinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng