Gwamna Zulum ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram

Gwamna Zulum ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram

- Gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum ya jadadda cewa akwai bukatar a sauya salon yakin da ake da yan ta’addan Boko Haram a kasar

- Zulum ya fadi hakan ne a gaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da ya kai ziyara garin Maidugurin ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu

- Shugaban kasar dai ya je Maiduguri ne domin mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’umman jahar Borno kan hare-haren da Boko Haram ta kai a Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30

Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno ya bayyana cewa akwai bukatar a sauya salon yakin da ake da yan ta’addan Boko Haram a kasar.

A cewar wata sanarwa daga hadimin Zulum a kafofin watsa labarai, Isa Gusau, gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Shehun Borno yayin da yake jawabi a gaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da ya kai ziyara garin Maidugurin ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Gwamna Zulum ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram
Gwamna Zulum ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram
Asali: Depositphotos

Shugaban kasar dai ya je Maiduguri ne domin mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’umman jahar Borno kan hare-haren da Boko Haram ta kai a Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30 tare da kona motoci 18 da kuma gidaje.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mutanen Borno sun yiwa Buhari ihun 'Bamayi' 'Bamaso' (Bidiyo)

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha.

Legit.ng ta rahoto cewa babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Ababa sannan a yanzun nan ya sauka a Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

Shugaban kasar zai kai ziyarar jaje ne ga gwamnati da mutanen jahar Borno biyo bayan mummunan lamarin da ya afku kwanan nan inda yan ta’addan Boko Haram suka kashe matafiya da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel