Yan Bindiga Sun Sauke Fushin Abin da Jami'an Tsaro Suka Musu kan Manoma a Sakkwato

Yan Bindiga Sun Sauke Fushin Abin da Jami'an Tsaro Suka Musu kan Manoma a Sakkwato

  • IAn kashe manoma akalla takwas, yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan ’yan bindiga sun kai hari Ghandi da ke karamar hukumar Rabah ta Sokoto
  • ’Yan bindigar sun mamaye garin da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Lahadi, inda suka rika harbin mazauna garin da manoma
  • Wani mazaunin yankin ya ce ana zargin harin ramuwar gayya ne bayan jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a wasu samame

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Wasu miyagun ’yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan manoma kauyen Ghandi da ke karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto a yammacin jiya Lahadi.

Akalla manoma takwas ne aka kashe, yayin da wasu biyar suka samu raunukan harbin bindiga bayan yan bindigar sun bude masu wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano, an sace babban mai rike da sarauta da kashe mutane

Taswirar jihar Sakkwato.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan sanda sun tabbatar da harin

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da harin yayin da yake zantawa da wakilin Tribune Nigeria ta wayar tarho a yammacin Lahadi.

Kakakin yan sandan ya ce maharan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 3:00 na yamma, inda suka rika harbin mazauna garin da manoma kafin daga bisani su tsere.

Rufai ya ce rundunar na sane da lamarin, inda ya kara da cewa za a fitar da karin bayani yayin da ake tantance halin da ake ciki, cewar rahoton Vanguard.

Ana zargi harin ramuwar gayya ne

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin na iya kasancewa ramuwar gayya ne sakamakon wasu samame da jami’an tsaro suka gudanar kan ’yan bindigar a baya-bayan nan.

“’Yan bindigar sun kai hari kauyen da misalin karfe 3:00 na yamma sannan suka fara harbi. An kashe manoma takwas, yayin da wasu kusan biyar suka samu raunukan harbin bindiga,” in ji majiyar.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Ya kara da cewa ana kyautata zaton maharan sun kai wa al’ummar hari ne domin ramuwar gayya kan kashe wasu daga cikin yan dabar ’yan kungiyar ta su da jami’an tsaro suka yi a ’yan kwanakin nan.

Yan sanda.
Dakarun yan sanda suna sintirin tabbatar da tsaro a kan titin jihar Zamfara Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter
“Da alama wannan harin na ramuwar gayya ne saboda jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin ’yan kungiyar a yayin gudanar da samame a yankin,” in ji shi.

Lamarin ya kara jefa mazauna Ghandi da kauyukan da ke makwabtaka da shi cikin fargaba, yayin da ake kara nuna damuwa kan tsaron manoma da sauran mazauna yankin sakamakon sabbin hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar Sokoto.

An kashe malamin musulunci a Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Gidan Kare, inda suka kashe malamin addinin Musulunci tare da yin garkuwa da akalla mutane 10.

Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai Mallam Dan Manga, Shehu, tagwayen mata Hassana da Hussaina, Badaru, ‘ya’yan Mallam Ayuba guda biyu, Saratu da wasu mutum biyu.

Wani mazaunin Daddade, wata al’umma da ke kusa da Gidan Kare, ya ce marigayi Mallam Abubakar shi ne malamin addinin Musulunci da ya koyar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262