Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa

Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa

Fadar Shugaban kasa a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ziyarar kwanan nan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jahar Borno ya nuna cewa har yanzu yana da shahara da karbuwa, inda ta kara da cewa mazauna jahar sun yaba da abun da ya yi wajen magance ta!addanci a arewa maso gabas.

Shugaba Buhari ya ziyarci Maiduguri don yi masu jaje, biyo bayan hare-hare da yan ta’addan Boko Haram suka kai wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama a Audo da ke karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

A yayin ziyarar, shugaba Buhari ya ziyarci Gwamnan Jahar, Babagana Zulum da Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi.

Hadimin Shugaban kasa na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina, wanda ya bayyana a shirin Politics Today na Channels TV, ya ce dandazon jama’ar da suka tarbi shugaba Buhari na da matukar yawa sannan cewa yan tsirarun muryoyin da suka bijire ba abun damuwa bane.

Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa
Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

“Ba ma yiwa Hakan kallo a matsayin rashin karbuwa; idan kuka duba wadanda suka zo yiwa Shugaban kasar barka da zuwa daga filin jirgin sama har zuwa fadar sarkin Borno, suna da yawa.

“Wasu kimanin kaso 90 zuwa 95 cikin dari na ta daga tsintsiya sama sanbab suka yiwa Shugaban kasar maraba, muryoyin wasu yan tsiraru da suka bijire cikin dandazon jama’a ba abun damuwa bane, hakan ba sabon abu bane ga damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Bayelsa: Za a dawowa Jam’iyyar APC da nasararta - Inji Timipre

“Har Yanzu Shugaban kasar na samun karbuwa, da shahara kuma mutanen Borno sun san me ya yi; sun yaba da abun da ya yi ta bangaren magance ta’addanci,” in ji shi.

Kan yaki da ta’addanci, Mista Adesina ya yi bayanin cewa shugaba Buhari ya damu matuka saboda ya dauki rantsuwar kare rayuka da dukiyoyi a kasar.

A wani labarin kuma, mun ji cewa fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.

Daily Nigerian ta ruwaito lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel