Yadda rayuwata ta sauya sanadiyyar haduwa ta da Zulum - Malamar Firamare Obiageli

Yadda rayuwata ta sauya sanadiyyar haduwa ta da Zulum - Malamar Firamare Obiageli

Yayin da Obiageli Mazi, mai shekaru 54, wacce kuma ta shafe shekaru 31 tana aiki a jihat Borno, inda ya rage mata bai fi shekara biyar ba tayi ritaya, kuma babu abinda ta ajiye sanadiyyar wannan aiki da tayi, amma sai wani ikon Allah ya hada ta da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, inda ta bayyana cewa shine ya canja mata rayuwa baki daya.

Matar wacce take ‘yar asalin jihar Abia ce ta hadu da Zulum a ‘yan kwanakin da suka gabata. Gwamnan ya same ta a makarantar firamare ta Shehu Sanda Kyarimi dake cikin garin Maiduguri da misalin karfe 6:30 na safe, kuma yaji dadin jajircewarta akan aikinta. Ya bata makudan kudade sannan yayi mata karin girma zuwa mataimakiyar hedimasta.

Yadda rayuwata ta sauya sanadiyyar haduwa ta da Zulum - Malamar Firamare Obiageli
Yadda rayuwata ta sauya sanadiyyar haduwa ta da Zulum - Malamar Firamare Obiageli
Asali: Facebook

“Duniya baki daya ta ganni, mutane na ta kirana daga ko ina na kasar nan. Hatta daga kasar Amurka mutane sun ganni.

“Nagode mai girma gwamnan mu, Farfesa Babagana Umara Zulum,” Ms Mazi ta bayyanawa ma’aikacin jaridar The Nation a makarantar Shehu Sanda Kyarimi.

Ta ce: “Na hadu da gwamna a ranar 7 ga watan Janairun 2020, na zo makarantar karfe 6:28 na safe. Ina shirin sanya sunana a cikin littafin ma’aikata, sai na ga sun shigo cikin makarantar da misalin karfe 6:30.

“Daya daga cikinsu ya zo ya same ni, yake tambayata ni wacece, ko ni ce shugabar makarantar. Na ce masa a’a, ni malamar firamare ce dake koyar da ‘yan aji daya.

“Sai yace kuma kika zo da wuri haka, sai nace masa ai kullum haka nake sammako. Ya tambayeni inda nake zama na gaya masa Sheikh Zarma Street, Kumshe. Sai ya ce mini tare da gwamna suka zo, dan haka zai je yayi masa bayani.

“Kawai sai naga gwamnan ya tinkaro inda nake, sai na dauki jaka ta nayi wajen da yake da gudu, sai ya ce na tafi a hankali ba sai nayi gudu ba, na je na gaida shi da sauran abokanan tafiyarshi.

“Gwamnan ya tambayeni menene sunana? na gaya masa, ya tambayeni wacece ni kuma me nake yi a nan? na gaya masa ni malamar firamare ce ta aji daya.

KU KARANTA: Ran maza ya baci: Hatta jihar Legas akwai Boko Haram - Buratai ya mayar da martani kan harin Boko Haram

“Ya tambayeni inda nake zama, na gaya masa. Sai ya ce kuma kika zo nan karfe 6:30? Sai ya girgiza kai ya ce kin cancanci a baki kyauta. Ya kuma tambayeni daga wacce jiha nake na gaya masa jihar Abia.

“Bayan haka ya tambayeni wane irin takardu nake dasu, na gaya masa NCE, da kuma shekarar da na gama. Ya tambayeni albashina na sanar dashi dubu talatin da biyar (N35,000). Ya tambayeni shekaru nawa nayi ina aiki? Na gaya masa shekaru 31.

“Sai ya ce: N35,000, shekaru 31, dole ayi miki kyauta. Ya tambayeni kin san wanene ni? Na ce kwarai kuwa na sanka, kai ne gwamna. Sai yaje motarshi ya dauko mini kudi.

“Sai na durkusa ina yi masa godiya ya ce kada ki damu dole ayi miki kyauta. Wani mutumi ya fito daga motarshi ya karbi lambar waya ta, sai na bashi.

“Lokacin dana rike kudin da farko ban ma kalli kudin ba, lokacin da ‘yar uwata Amaka ta tambayeni nawa ne sai nace mata dubu goma ne ina jin.

“Ban san cewa yana da yawa ba, sai bayan na koma gida mutane suka fara kirana suna cewa kowa ya ganni a bidiyo, hatta a kasar Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel