INEC Ta Magantu kan Zargin Sauya wa Jam'iyyarsu Kwankwaso 'Yan Takara

INEC Ta Magantu kan Zargin Sauya wa Jam'iyyarsu Kwankwaso 'Yan Takara

  • Hukumar INEC ta musanta zargin da jam'iyyar NDC ta yi na cewa an cire sunayen 'yan takarar da ta gabatar domin zaben 2027
  • Jam'iyyar ta yi zargin cewa an ɗaura sunayen wasu mutane tara da ba ta amince da su ba a matsayin 'yan takararta na majalisar dokoki
  • A martanin da hukumar INEC ta yi, ta ce ba ta da ikon doka na zaɓar ɗan takara ko sauya wanda jam'iyyar siyasa ta gabatar mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta mayar da martani kan zargin da jam'iyyar NDC ta yi na cewa hukumar ta sauya sunayen 'yan takarar da jam'iyyar ta gabatar domin zaben 2027.

NDC ta zargi INEC da wasu jami'anta da ɗora sunayen wasu mutane da ba ta amince da su ba a matsayin 'yan takararta a wasu mazabun majalisar dokokin jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar NDC ta su Kwankwaso ta zargi INEC da sauya sunayen 'yan takararta

Farfesa Joash Amupitan
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joash Amupitan. Hoto: INEC
Source: Twitter

Jaridar Punch ta rahoto cewa Babban Sakataren Yaɗa Labarai kuma mai ba Shugaban INEC shawara kan kafafen yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya mayar da martani kan zargin a ranar Litinin.

Abin da INEC ta ce kan zargin

Oketola ya ce aikin zaɓe da gabatar da 'yan takara na jam'iyyun siyasa ne, yayin da INEC ke da alhakin gudanar da zaɓe bisa tanadin kundin tsarin mulki, dokar zaɓe da sauran ƙa'idoji.

Ya ce:

“Don kauce wa shakku, INEC ba ta zaɓar 'yan takara a madadin jam'iyyun siyasa. Zaɓar 'yan takara alhakin jam'iyyun siyasa ne, bisa bin kundin tsarin mulki, da sauran dokoki, ƙa'idoji da jagororin da suka dace.”

Ya ƙara da cewa shafin yanar gizo da INEC ta samar domin gabatar da bayanan 'yan takara ita ce hanyar da jam'iyyu ke amfani da ita wajen shigar da bayanan 'yan takararsu, ta hanyar bayanan shiga da hukumar ta ba su.

Kara karanta wannan

Daga karshe: 'Yan N-Power da gwamnatin Tinubu ta hana kudadensu sun yanke Atiku za su zaba a 2027

A cewarsa, duk wani aiki da aka gudanar a shafin ana adana shi, kuma ana iya tabbatar da shi ta hanyar bayanan hukumar da kuma tarihin ayyukan da aka gudanar a tsarin.

Karin bayani daga INEC

PM News ta wallafa cewa Oketola ya ce bayanan hukumar za su iya tabbatar da yadda da kuma daga ina aka shigar da sunan kowane ɗan takara.

Ya ce saboda haka bai kamata a yanke hukunci kan zargin cewa jami'an INEC sun “shigar da” wasu 'yan takara cikin jerin NDC bisa zato kawai ba, domin bayanai da takardun hukumar za su iya bayyana ainihin abin da ya faru.

Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a wajen taron NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

'Yan adawa na shirin haɗa kai

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu daga cikin jam'iyyun adawa sun tabbatar da halartar taron G-100 da ake sa ran gudanarwa a yau a Cibiyar Yar'Adua da ke Abuja.

ADC ta bayyana cewa manufar taron ba ita ce zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya ba, sai dai samar da tsarin haɗin gwiwa da zai ƙarfafa jam'iyyun adawa gabanin zaben 2027.

Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce taron zai mayar da hankali kan samar da hanyar haɗin kai tsakanin jam'iyyun adawa domin tunkarar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng